Firaministan kasar Sin Li Qiang, ya nazarci rahoton gwamnati tare da tattaunawa da wakilan jama’a da suka fito daga lardin Yunnan, a jiya Talata.
Firaminista Li Qiang wanda kuma mamban zaunannen kwamitin hukumar siyasa ta kwamitin kolin JKS ne ya jadadda cewa, shugaban kasar Sin Xi Jinping na ba da muhimmanci matuka kan bunkasuwar yankin. Ya ce ya kamata a tabbatar da umurnin da shugaban ya bayar dangane da harkokin raya yankin, kuma a yi amfani da fifikon da yankin ke da shi bisa ajandar da taron tattalin arziki na kwamitin kolin JKS ya tsayar da rahoton gwamnatin, ta yadda yankin zai shiga tsarin rayawa da daidaita harkoki baki daya tsakanin yankuna daban-daban, da ma ingiza samun bunkasuwa mai inganci. Ban da wannan kuma, a cewarsa, an raya sana’o’i na musamman dake da alaka da fifikon yankin bisa halin da ake ciki, da ma karfafa raya sana’ar samar da hajoji da aikin gona irin na kan tudu da sana’ar yawon bude ido. (Amina Xu)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp