Firaministan kasar Sin Li Qiang, ya ce a matsayin Sin na babbar kasa mai tasowa dake sauke nauyin dake wuyanta, ba za ta nemi wani sabon matsayi na musamman, ko fifiko yayin tattaunawar cimma matsaya ta yanzu, da ma ta nan gaba, dangane da harkokin kungiyar cinikayya ta duniya WTO.
Li, ya yi wannan tsokaci ne yayin taron manyan jami’ai dangane da shawarar nan ta tsarin shugabanci da Sin ta gabatar, a gefen babban taron MDD karo na 80 dake gudana yanzu haka.
A yau Laraba, ma’aikatar cinikayya ta Sin ta kira taron manema labarai, inda mataimakin ministan cinikayya na Sin Li Chenggang, ya bayyana wannan muhimmiyar matsaya ta Sin, a matsayin alkawari dake mayar da hankali ga yanayi da ake ciki a cikin gidan Sin, da ma alakarta da sauran sassan kasa da kasa.
Li Chenggang, ya ce hakan muhimmin mataki ne da Sin ta dauka da nufin goyon bayan cudanyar cinikayya tsakanin mabanbantan sassan kasa da kasa, da aiwatar da shawarar tsarin shugabanci na duniya, wanda zai ingiza salon cinikayya da zuba jari mai ‘yanci da ci gaba, wanda ke karkata ga karfafa zuciya, da shigar da kuzari a salon gudanar da sauye-sauye ga tsarin jagorancin raya tattalin arzikin kasa da kasa. (Mai fassara: Saminu Alhassan)














