An gudanar da bikin murnar cika shekaru 80 da kafuwar jam’iyyar Kwadago ta Koriya ta Arewa wato (WPK) a birnin Pyongyang daga daren ranar Alhamis 9 ga watan nan zuwa jiya Juma’a. Firaministan kasar Sin Li Qiang ya halarci bikin, inda ya kalli manyan wasannin kwaikwayo, da faretin soja da dai sauran shirye-shiryen da aka tsara domin bikin.
A yayin bikin, Li Qiang ya kuma yi shawarwari da babban sakataren kwamitin tsakiyar Jam’iyyar Kwaminis ta Kasar Vietnam To Lam, da shugaban jam’iyyar hadaddiyar Rasha Dmitry Medvedev, da dai sauransu.
Sa’an nan, da safiyar yau Asabar, Li Qiang ya gana da takwaransa Pak Thae Song a birnin Pyongyang. Yayin zantawar tasu Li Qiang ya ce a yayin ganawar shugaba Xi Jinping da shugaba Kim Jong Un cikin watan Satumba, sun cimma matsaya daya, kan yadda za a zurfafa dangantakar dake tsakanin jam’iyyun biyu da kuma kasashensu.
Li ya ce kasar Sin za ta ci gaba da nuna goyon baya ga jam’iyyar WPK, don ta bayar da jagoranci ga al’ummun kasar Koriya ta Arewa, wajen neman ci gaba bisa halin da kasar take ciki. A sa’i daya kuma, kasar Sin tana fatan karfafa hadin gwiwa tsakanin kasashen biyu a fannoni da dama, kamar aiwatar da ra’ayi daya da shugabannin kasashen biyu suka cimma, tare da kara musayar manyan jami’ai, da mu’amala kan manyan tsare-tsare, ta yadda za a inganta fahimtar siyasa a tsakanin kasashen biyu, tare da cimma sakamako mai kyau bisa hadin gwiwar dake tsakanin Sin da Koriya ta Arewa. (Mai Fassara: Maryam Yang)