Bisa gayyatar da firaministan Pakistan Muhammad Shahbaz Sharif ya yi masa, firaministan kasar Sin Li Qiang ya isa birnin Islamabad da tsakar ranar jiya Litinin 14 ga wantan nan bisa agogon wurin ta jirgin sama, don fara ziyarar aiki a Pakistan a hukumance, tare da halartar taron kwamitin shugabannin gwamnatocin kasashe mambobin kungiyar SCO karo na 23.
Li Qiang ya bayyana cewa, bangaren Sin na fatan ci gaba da sada zumunta tare da bangaren Pakistan, da zurfafa hadin gwiwa na cimma moriyar juna, da raba damammakin bunkasuwa tare, ta yadda za a gina makoma mai kyau ta samun alherai, da ci gaba tare tsakanin kasashen biyu.
- Gwamnan Kebbi Ya Kaddamar Da Aikin Titi A Garin Argungu Kan Kudi Fiye Da Naira Biliyan 7.2
- Sin Ta Gabatar Da Alkaluman Cinikin Shige Da Fice Na Watan Jarairu Zuwa Satumba Na Bana
Li Qiang ya kara da cewa, bangaren Sin na fatan aiwatar da sakamakon da aka cimma yayin taron kolin Astana, da ci gaba da yada “ruhin Shanghai”, da zurfafa hadin gwiwa a dukkan fannoni, da inganta kungiyar SCO ta hada karfin bangarori daban daban, ta yadda za a taka muhimmiyar rawa ga bunkasa zaman lafiya da kwanciyar hankali, da kuma bunkasuwa a yankin.
A dai jiyan, Li Qiang ya gana da firaministan Shahbaz a fadarsa dake Pakistan, sun kuma halarci bikin kammala aikin gina sabon filin jirgin saman Gwadar tare. (Safiyah Ma)