Yayin da sabuwar shekarar gargajiya ta kasar Sin ko Bikin Bazara ke karatowa, firaministan kasar Sin Li Qiang ya gana da wakilan kwararru ‘yan kasashen waje da suka samu lambar yabo ta abota ta gwamnatin kasar Sin, wadanda kuma suka yi aiki a kasar, a babban dakin taron al’umma da yammacin yau Lahadi, inda suka tattauna tare da yin musayar ra’ayi.
Li Qiang ya mika gaisuwar sabuwar shekara da fatan alheri ga kwararrun da iyalansu, yana mai gode musu game da kulawa da goyon bayan da suka dade suna ba ci gaban kasar Sin tare da sauraron ra’ayoyi da shawarwarinsu kan ayyukan gwamnati da na raya kasar.
Li Qiang ya bayyana cewa kofar ci gaban kasar Sin a bude take, kuma tana maraba da kwararru daga fadin duniya da hannu bibbiyu. Ya kara da cewa, suna fatan kwararrun za su ci gaba da shiga ana damawa da su a ayyukan raya kasar, da baje kwarewarsu a babban dandalin tafarkin zamanantar da kasar Sin, da kuma ci gaba da zama gadar sada zumunci tsakanin Sin da sauran sasssan duniya. (Fa’iza Mustapha)