Li Qiang ya yi nuni da cewa, a kwanakin baya, kasar Amurka ta sanar da kara buga harajin kwastam ga dukkan kasashe abokanta na cinikayya ciki har da Sin da Turai, wanda mataki ne da bangare daya ya dauka, da ba da kariya ga cinikayya, da cin zarafin tattalin arziki. Ya ce, kasar Sin ta dauki matakai don tabbatar da ikon mulkinta da moriyar samun ci gaba cikin aminci, kana da tabbatar da ka’idojin cinikayya da adalci a duniya. Ya kara da cewa, ya kamata Sin da Turai su kara mu’amala da juna, da bude kofa ga juna don tabbatar da yin ciniki da zuba jari cikin ‘yanci, da kiyaye tsarin samar da kayayyaki a duniya yadda ya kamata, ta yadda za su kara tabbatar da bunkasuwar tattalin arzikinsu da na duniya baki daya.
A nata bangare, Ursula von der Leyen ta bayyana cewa, matakan kara buga harajin kwastam na kasar Amurka sun kawo illa ga cinikayya tsakanin kasa da kasa, tare da yin mummunan tasiri ga kasashen Turai da Sin da sauran kasashe marasa karfi. Ta ce, bangarorin Turai da Sin sun yi kokarin tabbatar da tsarin yin ciniki tsakanin bangarori daban daban bisa tushen WTO da adalci da ‘yanci, da kiyaye bunkasa huldar tattalin arziki da cinikayya a tsakanin kasa da kasa yadda ya kamata, lamarin da ya dace da moriyar bangarorin biyu har ma da ta duk duniya baki daya. (Zainab Zhang)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp