Firaministan kasar Sin Li Qiang ya jaddada yayin ziyararsa a lardin Hainan na kasar Sin cewa, ya kamata a kiyaye yin kwaskwarima a gida da bude kofa ga kasashen waje, da raya tashar jiragen ruwan ciniki cikin ‘yanci mai inganci a lardin Hainan. Ya yi nuni da cewa, ya kamata a raya ayyukan fannoni daban daban da inganta karfin yin hadin gwiwa da sa ido ga ayyukan lardin don aza tubalin mai da tsibirin Hainan matsayin yankin da hukumar kwastam ke tafiyar da harkokinsa a karshen shekarar 2025.
Bisa tsarin da aka tsara, a shekarar 2025, za a kafa tsarin manufofin tashar jiragen ruwan ciniki cikin ‘yanci a lardin Hainan, ta yadda za a fi mai da hankali ga yin ciniki da zuba jari cikin ‘yanci.
Firaministan kasar Sin Li Qiang ya bayyana yayin da yake ganawa da shugabar asusun ba da lamuni na duniya wato IMF Kristalina Georgieva a birnin Boao dake lardin Hainan a yau cewa, Sin ta yi imani da karfinta wajen cimma burin samun bunkasuwa a shekarar bana. Ya jaddada cewa, ya kamata kasa da kasa su kiyaye ra’ayin bangarori daban daban don tabbatar da samar da kayayyaki a duk duniya yadda ya kamata.
A nata bangare, Kristalina Georgieva ta bayyana cewa, ana sa ran cewa, Sin za ta samar da gudummawar fiye da kashi daya cikin kashi uku na bunkasuwar tattalin arzikin duniya. Kuma asusun IMF ya yabawa kasar Sin domin ta kiyaye ra’ayin bangarori daban daban da samar da gudummawa wajen magance kalubalen basussuka ga kasashe masu tasowa, kana IMF yana son kara yin hadin gwiwa tare da kasar Sin. (Zainab)