Kakakin ma’aikatar kula da harkokin kasuwanci ta kasar Sin, He Yadong ya sanar da cewa, za a gudanar da taron CIIE karo na 8 a birnin Shanghai daga ranar 5 zuwa ta 10 ga watan Nuwamba. Kuma firayim ministan kasar Sin Li Qiang zai halarci bikin bude taron da sauran ayyukan tare da gabatar da wani jawabi. (Amina Xu)
			




							








