Rundunar ‘yansandan Jihar Kano ta samu gagarumar nasara a kokarinta na tabbatar da adalci, inda ta sanar da kama wasu masu mutum biyu da laifukan kisan kai a jihar.
A ranar 20 ga watan Disamba, 2023, Nura Balarabe ya ruwaito cewa Ukasha Muhammed, mai shekaru 19, ya yi wa ‘yar uwarsa, Amina Bala ciki.
- An Kashe Sama Da Mutane 100 A Harin Bam A Iran
- Cire Tallafin Fetur: Kano Za Ta Biya Ma’aikata Karin Albashin N20,000, ‘Yan Fansho N15,000.
Wadanda ake zargin, Ukasha Muhammed da Chidera Ugwu mai shekaru 24, sun hada baki wajen yi wa Amina allurar zubar da ciki.
Lamarin dai ya yi sanadin mutuwar Amina nan take.
Kwamishinan ‘yansandan jihar, CP Mohammed Usaini Gumel, ya tabbatar wa da jama’a kudurin rundunar na gudanar da cikakken bincike kan lamarin.
Gumel ya yi wa jama’ar jihar godiya kan irin goyon bayan da suke bai wa rundunar.
Ya kuma bukaci jama’a da suke kai rahoton faruwar laifuka ofishin ‘yan sanda mafi kusa da su.
Kwamishinan ya jaddada muhimmancin hadin gwiwa wajen tabbatar da doka da oda a jihar
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp