Sama da mutane 100 ne suka rasa rayukansu a wani harin bam guda biyu da aka kai kan jama’ar da suka yi dandazo a Iran domin tunawa da marigayi Janar Qassem Soleimani da Amurka ta kashe shi a wani harin jirgi mara matuki.
Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da ake zaman dari-dari a yankin gabas ta tsakiya sakamakon yakin Isra’ila da Hamas a Zirin Gaza.
- Juyin Mulki: Faransa Ta Rufe Ofishin Jakadancinta Na Nijar
- Mutane 6,000 Sun Amfana Da Zakka Ta Miliyan N132 A Masarautar Hadejia – Kakakin Masarautar
Harin na wannan Laraba, ya auku ne a kusa da kabarin marigayin da ya kasance shugaban da ke kula da ayyukan dakarun juyin-juya-halin Iran a Masallacin Saheb al-Zaman da ke birnin Kerman a yankin kudancin kasar.
Tuni matakimakin gwamnan Lardin Kerman, Rahman Jalali ya bayyana wannan harin a matsayin ta’addanci.
Shekaru hudu kenan da mutuwar Soleimani wanda harin na jirgin Amurka mara matuki ya kashe shi a birnin Bagdad na Iraq.
Kawo yanzu babu wata kungiya da ta dauki alhakin kaddamar da farmakin kan jama’ar na Iran.
Ko da yake Isra’ila ta kai jerin hare-hare kan wasu daidaikun mutane a Iran saboda shirin nukiliyar kasar, amma ba ta taba kai hari kan taron jama’a ba.
Kungiyoyin masu tsattsauran ra’ayi irinsu IS sun sha kaddamar da hare-hare a baya da suka yi sanadiyar mutuwar fararen hula a yankin da mabiya akidar Shi’a ke da rinjaye a Iran.