Ƙungiyar Likitocin Masu Neman Ƙwarewa a Nijeriya (NARD) ta tsunduma cikin yajin aikin ƙasa baki ɗaya, bayan gwamnatin tarayya ta kasa cika mafi ƙarancin bukatun da ƙungiyar ta gabatar cikin wa’adin sa’o’i 24 da ta sanya. Wannan mataki ya zo ne bayan kammala taron gaggawa na Majalisar Zartarwa ta Ƙasa (E-NEC) ta yanar gizo a ranar Laraba, 10 ga Satumba, 2025.
Shugaban ƙungiyar na ƙasa, Dakta Osundara Tope Zenith, ya tabbatar da hakan, inda ya ce yajin aikin ya zama dole bayan shiru daga bangaren gwamnati. Ƙungiyar ta jaddada cewa rashin biyan Kudaden Tallafin Koyan Aiki (MRTF) ga wasu asibitoci, tare da rashin biyan alawus na watanni biyar daga karin kaso 25% da 35%, da sauran hakkoki da aka dakatar ko aka ki biya, ya zama babban dalilin yajin.
- Likitoci Sun Fara Yajin Aikin Gargaɗi Na Mako Ɗaya A Abuja
- Likitoci Sun Gano Wuka Da Aka Burma A Kirjin Wani Mutum Tsawon Shekara 8
Masu sharhi na ganin cewa wannan yajin aikin na iya kawo tsaiko a harkar lafiya a fadin Nijeriya, musamman ganin cewa yawancin asibitocin gwamnati suna dogaro da likitocin masu neman ƙwarewa wajen gudanar da ayyukan yau da kullum. Rashin wadannan likitoci na nufin jama’a za su fuskanci cikas wajen samun kulawar lafiya da gaggawa.
Hakan ya sa ake kira ga gwamnati da ta gaggauta shiga tattaunawa da NARD domin kawo karshen wannan rikici, ganin cewa jinkiri na iya jefa rayukan marasa lafiya cikin haɗari. Yajin aikin ya sake bude babin tattaunawa kan matsalolin da ke addabar tsarin kiwon lafiya a Nijeriya da kuma yadda ake tafiyar da hakkokin ma’aikata.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp