Ƙungiyar Likitoci masu neman ƙwarewa (Resident Doctors) a ƙarƙashin Hukumar Kula da Birnin Tarayya (ARD-FCTA) ta sanar da shiga yajin aiki na dindindin bayan ƙarewar yajin aikin gargaɗi na kwana bakwai da suka fara tun 8 ga Satumba, 2025.
Wannan mataki ya fito ne a cikin wata sanarwa da shugabannin ƙungiyar, Dr. George Ebong (Shugaba) da Dr. Agbor Affiong (Sakataren Ƙoli), suka sanya wa hannu a safiyar Litinin.
- PDP Ta Dage Kan Gudanar Da Taronta Duk Da Sabbin Sharuɗɗan Da Ɓangaren Wike Ya Gindaya
- Majalisa Ta Bai Wa Minista Sa’o’i 48 Ya Bayyana A Gabanta Kan Hatsarin Jirgin Abuja Zuwa Kaduna
Ƙungiyar ta bayyana Ƙorafe-ƙorafen da suka shafi biyan bashin albashi tsakanin wata 1 zuwa 6 ga likitocin da aka ɗauka tun 2023, rashin biyan kuɗin atisaye (Medical Residency Training Fund (MRTF)) na 2025, jinkirin ƙarin matsayi, da ci gaba da rage musu albashi ba bisa ƙa’ida ba.
Haka kuma, sun koka da rashin ɗaukar sabbin likitoci duk da ƙarancin ma’aikata a asibitocin FCT, abin da suka ce ya haddasa mutuwar wasu ma’aikatan lafiya saboda gajiya da damuwa, tare da jefa lafiyar marasa lafiya da likitoci cikin “babban haɗari mai iya zama bala’i.”
ARD-FCTA ta jaddada buƙatunta da suka haɗa da biyan dukkan bashin albashi, da ɗaukar sabbin likitoci kafin ƙarshen 2025, biyan cikakken alawus na MRTF, da kuma gyaran asibitocin FCT cikin gaggawa. Sun kuma bukaci a ayyana dokar ta baci a asibitocin FCT, inda suka ce babban birnin ƙasar da ya kamata ya zama abin koyi a kiwon lafiya ya koma “ƙasa da matsayin da ya dace da shi.”
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp