A bana ne ake cika shekaru 60 tun bayan da kasar Sin ta fara aikewa da jami’an kiwon lafiya masu aikin jin kai zuwa kasashen Afirka daban daban. A sassa da dama a nahiyar Afirka, tawagogin likitocin na Sin sun yi rawar gani, wajen taimakawa mazauna wuraren, har ta kai ana kiran su da “Wakilai na gari kuma jakadun wanzar da kawance”, matsayin da ko shakka babu ya dace da godiyar da al’ummun nahiyar ke yiwa wadannan jami’ai masu aikin sadaukar da kai.
Tun bayan aikewa da tawagar irin wadannan likitoci na Sin zuwa kasar Aljeriya a watan Afrilun shekarar 1963, Sin ta ci gaba da aikewa da tawagogi daban daban zuwa Afirka. Baya ga kayan aiki da horaswa a fannin sanin makamar aiki da tawagogin ke samarwa a nahiyar.
Cikin sama da shekarun nan 60, Sin ta aike da tawagogin tallafin jinya mai kunshe da jimillar mambobi 30,000 zuwa kasashe da yankunan duniya 76, a sassan nahiyoyin duniya 5. Wasu alkaluman sun nuna cewa, adadin marasa lafiya da rukunonin likitocin Sin masu aikin jin kai suka yiwa jinya ya kai miliyan 290. Kaza lika a yanzu haka, wasu tawagogin likitocin na Sin na aiki a wurare 115 dake kasashe 57, kuma kusan rabin su na aiki ne a wurare masu wuyar kaiwa da yanayi mai tsanani.
Sanin kowa ne cewa nahiyar Afirka na shan fama da cututtuka masu yaduwa, kamar zazzabin cizon sauro ko Malaria, da Amai da gudanawa, da zazzabin shawara da sauran su, cututtukan da masana ke cewa karancin ababen more rayuwa ta fuskar kiwon lafiya, da kwararrun jami’an lafiya ne ke kara ta’azzara yaduwar su. Don haka ne ma rukunonin likitocin da Sin ke turawa suka dukufa, wajen samar da jinya ga dubun dubatar al’ummun nahiyar masu bukatar taimako.
Ko shakka babu rukunonin likitocin Sin sun cancanci yabo, bisa yadda suka gudanar da aikin tiyatar zuciya irin sa na farko a kasar Sudan, da dashen na’urar taimakawa zuciya irin sa na farko a Gambia, da aikin kwakwalwa irin sa na farko a kasar Benin, da dashen kafada a Mozambique da dai sauran su.
Cikin wadannan shekaru 60 da Sin ta shafe tana agazawa nahiyar Afirka ta fuskar kiwon lafiya, al’ummun nahiyar na ta jinjinawa moriyar da suka samu daga wannan aiki. Kuma a wannan gaba da Sin da kasashen Afirka ke kokarin gina al’umma mai makomar bai daya a sabon zamani, ciki har da fannin kula da lafiyar al’umma, tabbas likitocin Sin dake halartar ayyukan tallafawa al’umma a Afirka, na kan gaba wajen taimakawa cin nasarar wannan manufa.(Saminu Alhassan)