Shahararren dan kwallon kafa na kasar Argentina mai taka leda a kungiyar Inter Miami ta kasar Amurka Lionel Messi. Ya lashe kyautar gwarzon dan kwallon kafa ta Ballon D’or a karo na takwas a tarihi.
Ana hasashen kyautar zata tafi wurin dan wasan gaban Manchester City Erling Haaland amma abin mamaki Messi ya kuma lashewa.
Messi ya yi takara ne da Erling Haaland (Manchester City) da Kevin De Bruyne (Manchester City) da Kylian Mbappe (PSG)
Messi ya koma kungiyar Inter Miami ne daga kungiyar PSG