Shugaban kasa, Muhammadu Buhari, a ranar Litinin a garin Yola ta jihar Adamawa, ya ce, zabin Sanata Aisha Dahiru Ahmed Binani a matsayin Gwamnan Jihar a zaben 2023 da ke tafe zai bude sabon babi da ga ‘yan uwa mata a fadin kasar.
Buhari ya ce, yanzu fa ya kamata a bai wa mata gurabe su ma su fito a dama da su a bangaren gudanar da shugabanci a kasar nan.
- An Sulhunta: Nuhu Ribadu Ya Hakura, Ya Bar Wa Aisha Binani Takarar Gwamnan APC A Adamawa
- Kotun Daukaka Kara Ta Dawo Wa Da Aishatu Binani Takararta Ta Gwamna A Adamawa
Da yake jawabi a fadar Lamidon Adamawa a garin Yola, Shugaban kamar yadda da Kakakinsa Femi Adesina ya nakalto, ya ce, zai taimaka wa takarar Binani dari bisa dari kuma zai ci gaba da ba ta kwarin guiwa kan wannan matakin na neman gwamna da take yi.
“Mun zo nan ne domin mu tabbatar Sanata Binani ta zama zababbiyar gwamna ta farko da izinin Allah. Zabinta tamkar isar da sako ne ga Nijeriya da ma kasashen duniya.
“Ina muku godiya matuka a kan dukkan goyon bayanku. Ina fatan dukkaninku za ku goya mata baya ta kai ga nasara. Ga sauran ‘yan takara da suke bangaren adawa kuwa, ina musu fatan alheri.”
A nasa jawabin, gwamnan Jihar Adamawa, Ahmadu Umaru Fintiri, ya gode wa shugaban kasa Muhammadu Buhari bisa ayyukan da ya shimfida a jihar daban-daban.
“Muna yi wa Shugaban kasa godiya kan ayyuka daban-daban da aka gudanar a jihar Adamawa. Za mu ci gaba da maka addu’a. .
“Ka yi matukar kokari sosai don ka yi abubuwa fiye da yadda ake tsammani a matsayinka na shugaba. Ina maka fatan alheri da fatan a kammala dukkanin yakin neman zabe cikin nasara,” cewar gwamnan.
Lamidon Adamawa, Alhaji Muhammadu Barkindo Aliyu Mustapha, shi ma godiya ya yi wa shugaban kasa bisa ayyukan raya jihar da ya gudanar.
Ya kuma yaba masa bisa irin nade-naden mukamai da ya bai wa ‘yan asalin jihar a cikin gwamnatinsa da suka hada da ministan babban birnin tarayya Abuja, Mohammed Musa Bello, sakataren Gwamnatin tarayya, Boss Mustapha da kuma shugaban hukumar yaki da fataucin miyagun kwayoyi NDLEA, Buba Marwa.
Sarkin ya kuma gode wa shugaban kasa Buhari kan amincewa da gina sabbin jami’o’i a jihar.