Mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima ya jajanta wa jama’a da gwamnatin jihar Enugu kan gobarar tankar mai da ta yi sanadin salwantar rayuka a jihar, inda ya ce lokaci ya yi da za a kawo karshen hadurran tankar mai.
A ranar Asabar din da ta gabata ne wata tankar man fetur ta kama da wuta inda ta kone kurmus a kan hanyar Ugwu-Onyeama ta babbar hanyar Enugu zuwa Onitsha.
- ‘Yan Bindiga Sun Sace Magidanci Da Iyalansa Da Makwabta A Abuja
- Shugabannin Sin Sun Mika Gaisuwar Bikin Bazara Ga Tsoffin Jami’ai Da Suka Yi Ritaya
A sakon ta’aziyya ga iyalan wadanda suka rasa rayukansu da wadanda suka jikkata, mataimakin shugaban kasar, a wata sanarwa da mai magana da yawunsa, Stanley Nkwocha, ya fitar a ranar Lahadi, ya bayyana cewa, shugaba Bola Tinubu ya damu matuka da yadda tankokin man fetur ke yawan samun hadurra a ‘yan kwanakin nan.
Shettima ya yi alkawarin cewa, bisa umarnin shugaban kasa, gwamnati za ta hada hannu da hukumomin da abin ya shafa, ciki har da hukumar kiyaye hadurra ta kasa (FRSC), kan hanyoyin da hukumomin kula da zirga-zirgar ababen hawa, da ma’aikatun sufuri na tarayya da na Jihohi za su hada kai don dakile yawaitar hadurran tankar mai a fadin kasar.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp