Wata manhaja da ake kira “Red Note” ta kasar Sin, ta shahara sosai kwanakin baya a Amurka. Wadda ta kai matsayin farko a bangaren sada zumunta da ake saukewa daga dandalin sauke manhajoji na sassan arewacin nahiyar Amurka na kamfanin Apple.
Masu amfani da yanar gizo na Sin da Amurka, suna farin ciki da yin mu’ammala sosai kan wannan manhaja a bangaren dabbobin gida, da salon kayan sawa, da abinci da sauransu.
- Za A Kammala Aikin Titin Abuja-Kaduna-Kano Cikin Watanni 14 – Gwamnati
- Za Mu Kalubalanci Duk Wani Yunkuri Na Mayar Da Nijeriya Tsarin Jam’iyya Daya – PDP
Muhimmin dalilin da ya sa wannan manhaja ke kara shahara a Amurka, shi ne yiwuwar gwamnatin Amurka ta katse manhajar “TIKTOK” a kasar, tun daga ranar 19 ga wannan wata da muke ciki, bisa barazanar cewa, idan ba a yarda da sayar wa kasar Amurka manhajar ba, gwamnatin kasar Amurka za ta rufe ta baki daya.
Wasu Amurkawa masu amfani da TIKTOK, sun rubuta a kan yanar gizo cewa, ba su fahimci dalilin da ya sa gwamnatinsu ke tuhumar TIKTOK da haifar da barazana ga tsaron kasar ba, suna fatan “Red Note”, zai zama wani sabon dandalin musanyar al’adu tsakanin al’ummun kasashen biyu.
Shaharar “Red Note” a Amurka, ya bayyana matukar bukatar al’ummun Sin da Amurka na kara cudanya tsakaninsu. ’Yan siyasar Amurka ba za su iya hana cudanyar al’ummun kasashen biyu ba, duk da cewa suna iyakacin yunkurin shafawa kasar Sin bakin fenti, da matsa mata lamba kan bunkasuwarta.
Sabuwar gwamnatin Amurka za ta kafu nan da kwanaki masu zuwa. Sin na fatan manyan jami’an Amurka za su saurari ra’ayin al’ummun biyu, na fatan kara mu’ammala da sada zumunta, da bin hanya daya da kasar Sin, don shimfida wata hanyar da ta dace ga cudanyar jama’ar kasashen biyu, matakin da zai gaggauta tabbatar da huldarsu da samun ci gaba. (Amina Xu)