Dan wasan tawagar Super Eagles ta Nijeriya, Ademola Lookman yana gaba a cikin jerin ‘yan takara biyar a kyautar gwarzon dan kwallon kafar Afirka na bana da ake bayarwa duk shekara ga dan wasan da ya fi bajinta.
Hukumar Kwallon Kafar Afirka, CAF ce ta bayyana sunayen ‘‘yan wasan ranar Litinin da ake sa ran fayyace gwarzon bana duk da cewa a cikin jerin ‘yan wasan da aka fitar kowanne daga cikinsu kwaarre ne a kwallon kafa.
- Hanyoyin Da Mata Za Su Bi Don Gyara Jikinsu
- Gwamnan Edo Ya Kafa Kwamitin Mutum 14 Don Binciken Tsohon Gwamnan Jihar
Lookman ya ci kwallo uku a wasan karshe a Europa League da ta kai Atalanta ta lashe kofin, bayan doke kungiyar kwallon kafa ta bayer Liberkusen, sannan ya taka rawar gani da Super Eagles ta samu gurbin shiga gasar kofin Afirka da za a yi a badi.
Yana takara tare da dan kasar Morocco, Achraf Hakimi, wanda ya lashe Ligue 1 a Paris St Germain da dan kasar Guinea, Serhou Guirassy, wanda ya ci kwallo 28 a Bundesliga a kakar da ta wuce a Stuttgard, hakan ya sa Borussia Dortmund ta saye shi.
Sauran sun hada da Simon Adinga mai buga wasa a kungiyar kwallon kafa ta Brighton & Hobe Albion, wanda ya buga gasar da Ibory Coast ta lashe kofin Afirka da mai tsaron ragar Afirka ta Kudu, Ronwen Williams.
Masu koyarwa na kasashe 54, wadanda suke mamba a hukumar kwallon kafar Afirka ke yin zaben tare da wasu kwararrun kuma ana sa ran bayyana gwarzon dan kwallon kafar Afirka na bana ranar 16 ga watan Disamba a Birnin Marrakech na kasar Morocco.