Kungiyar kwallon kafa ta Inter Milan tana ci gaba da tattaunawa da Rumelu Lukaku domin daukar dan wasan a matsayin aro na shekara daya kamar yadda babban jami’in kungiyar, Giuseppe Marotta ya sanar.
Dan wasa Lukaku dan tawagar Belgium mai shekara 29, ya ci kwallo 15 a dukkan wasannin da ya yi wa Chelsea a kakar da aka kammala har da takwas a karawa 26 a Premier League bayan ya koma kungiyar .kan fam miliyan 97.5.
Lukaku, wanda ya bar Chelsea zuwa Everton kan kudi fam miliyan 28 a shekarar 2014, ya sake komawa Chelsea daga Inter a matakin wanda ta saya mafi tsada cikin watan Agustan shekara ta 2021 kan kwantiragin kaka biyar.
A kakar wasan data gabata ne dai Lukaku ya bayyanawa manema labarai a kasar Ingila cewa yana kewar kungiyar Inter Milan kuma yana fatan watarana zai sake komawa domin ya ci gaba da buga mata wasa.
Haka kuma jami’in ya sanar cewar suna kan batun daukar tsohon dan wasan Juventus Paulo Dybala da dan wasan Roma, Henrikh Mkhitaryan da mai tsaron ragar tawagar Kamaru, Andre Onana daga Ajax.
Dan wasan tawagar Argentina, Dybala, mai shekara 28, zai kasance wanda bai da yarjejeniya a karshen watan nan kuma tuni ya amince da albashin da kungiyar zata bashi.
Kungiyar Inter Milan ta kammala a mataki na biyu a Serie A a kakar da aka kammala da tazarar maki biyu tsakaninta da abokiyar adawarta, AC Milan wadda ta dauki kofin a karon farko tun bayan shekara 11.