Ƙungiyar ƙwallon kafa ta Luton Town ta koma gasar Championship mai daraja ta biyu ta ƙasar Ingila bayan da abokiyar karawarta Fulham ta doke ta da ci 4-2 a ranar Lahadi a wasan da suka buga a filin wasa na Kenilworth Stadium.
Luton ta dawo buga gasar Firimiya a wannan kaka da aka kammala bayan da ta doke ƙungiyar ƙwallon kwallon kafa ta Coventry a wasannin Play Off.
- Arsenal Ta Sake Tabbatar Da Cancantar Lashe Firimiya
- Hidimta Wa Al’umma Shi Ne Babban Burina -Injiniya Hassan
Amma yanzu kuma zata koma inda ta fito bayan ta kare a matsayi na 18 da maki 26 bayan buga wasanni 38 a wannan kakar, amma kocin ƙungiyar Rob Edwards ya yaba da kokarin da yan wasansa suka yi inda ya godewa mahukunta da magoya bayan ƙungiyar.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp