ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Wednesday, November 12, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Ma’aijin PDP Na Arewa Maso-Gabas Ya Fice Daga Jam’iyyar Kan Zargin Yi Wa Wike Rashin Adalci

by Khalid Idris Doya
3 years ago
PDP

Ma’ajin jam’iyyar PDP a shiyyar arewa maso gabas, Hon. Galadima Abba Itas ya fice daga jam’iyyar tare da yasar da katin shaidar zamansa mambar jam’iyyar a jihar Bauchi bisa abun da ya zarga na rashin adalci wa gwamnan Ribas Nyesom Wike.

A wasikar fita daga jam’iyya da ya aike wa shugaban PDP a gundumar Itas da ke karamar hukumar Itas/Gadau a jihar Bauchi wanda LEADERSHIP Hausa ta ci karo da kwafinta, Hon. Abba ya shaida cewar ajiye shaidar zama dan jam’iyyar ya biyo bayan shawara da tuntubar masu ruwa da tsaki a siyasance da kuma abokai ne, inda suka amince masa da ya dauki wannan matakin.

  • Dubban Mambobin Jam’iyyar APC Sun Sauya Sheka Zuwa Jam’iyyar PDP A Bauchi

Hon. Galadima Abba ya danganta ficewarsa daga PDP bisa abun da ya kira rashin adalcin da jam’iyyar ta yi wa gwamnan jihar Ribas Barista Nyesom Ezenwo Wike gabanin da kuma bayan zaben fitar da gwanin dan takarar shugaban kasa.

ADVERTISEMENT

“Don haka zabin da aka yi wa Gwamna Ifeanyi Okowa a matsayin mataimakin dan takarar shugaban kasa na PDP sun saba wa ka’idojin siyasana da kuma akidata don haka na ga dacewar fita daga jam’iyar,” Inji Abba.

Ya ce, a matsayinsa na daya daga cikin masu ruwa da tsaki na jam’iyyar, ya gano cewa, rashin adalci ga mambobin da suka kafa jam’iyyar na barazana ga siyasar jagororin jam’iyyar a kashin kansu, don haka ya zama masa dole ya fice daga jam’iyyar domin nuna rashin gamsuwarsa bisa abubuwan da ake yin a rashin adalci a cikin PDP.

LABARAI MASU NASABA

Majalisar Wakilai Ta Yi Tir Da Harin Da Aka Kai Wa Tawagar Ɗan Majalisar Neja

Dalilin Da Ya Sa Sanatoci Ba Su Goyi Bayana Ba Lokacin Da Aka Dakatar Da Ni – Natasha

A cewarsa, halin da ake ciki a jam’iyyar PDP na matukar barazana ga yunkurin PDP na kwace mulki daga hannun APC a 2023, ya kuma gode da irin dammar da jam’iyyar ta ba shi, don haka ya shelanta wa duniya barin PDP.

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Majalisar Wakilai Ta Yi Tir Da Harin Da Aka Kai Wa Tawagar Ɗan Majalisar Neja
Labarai

Majalisar Wakilai Ta Yi Tir Da Harin Da Aka Kai Wa Tawagar Ɗan Majalisar Neja

November 7, 2025
Dalilin Da Ya Sa Sanatoci Ba Su Goyi Bayana Ba Lokacin Da Aka Dakatar Da Ni – Natasha
Siyasa

Dalilin Da Ya Sa Sanatoci Ba Su Goyi Bayana Ba Lokacin Da Aka Dakatar Da Ni – Natasha

November 4, 2025
“Ƴan Adawa Sun Wuce Gona da Iri — Wike Ya Soki Masu Goyon Bayan  Trump
Labarai

“Ƴan Adawa Sun Wuce Gona da Iri — Wike Ya Soki Masu Goyon Bayan  Trump

November 3, 2025
Next Post
Har Gobe Nijeriya Ta Fi Yadda Take A 2015 – Fadar Shugaban Kasa

Har Gobe Nijeriya Ta Fi Yadda Take A 2015 - Fadar Shugaban Kasa

LABARAI MASU NASABA

Coas

Bayan Ganawa Da Tinubu, COAS Ya Tabbatar Wa ‘Yan Nijeriya Samun Ingantaccen Tsaro

November 11, 2025
Sin: Amurka Ba Ta Sa Lura Ga Kare Hakkin Dan Adam

Sin: Amurka Ba Ta Sa Lura Ga Kare Hakkin Dan Adam

November 11, 2025
Bikin CIIE Ya Nuna Yadda Sin Ke Ba Da Jagora Kan Harkokin Bude Kofa

Bikin CIIE Ya Nuna Yadda Sin Ke Ba Da Jagora Kan Harkokin Bude Kofa

November 11, 2025
Za Mu Ci Gaba Da Tallafa Wa ’Yansanda Domin Inganta Ayyukan Su A Zamfara – Gwamna Lawal

Za Mu Ci Gaba Da Tallafa Wa ’Yansanda Domin Inganta Ayyukan Su A Zamfara – Gwamna Lawal

November 11, 2025
CIIE Ya Kasance Gadar Sada Tattalin Arzikin Kasar Sin Da Na Duniya

CIIE Ya Kasance Gadar Sada Tattalin Arzikin Kasar Sin Da Na Duniya

November 11, 2025
CMG Ya Gabatar Da Sabbin Manhajoji 10 Da Ya Kirkiro Don Watsa Gasar Wasannin Motsa Jiki Ta Kasar Sin Karo Na 15

CMG Ya Gabatar Da Sabbin Manhajoji 10 Da Ya Kirkiro Don Watsa Gasar Wasannin Motsa Jiki Ta Kasar Sin Karo Na 15

November 11, 2025
‘Yan Bindiga Sun Kashe Mutum 3 A Nasarawa

‘Yan Bindiga Sun Kashe Mutum 3 A Nasarawa

November 11, 2025
Cikin Wata Ɗaya, ‘Yansanda Sun Kama Mutane 200 Da Ake Zargi Da Laifuka A Katsina

Cikin Wata Ɗaya, ‘Yansanda Sun Kama Mutane 200 Da Ake Zargi Da Laifuka A Katsina

November 11, 2025
CIIE Ya Ba ‘Yan Kasuwar Afirka Damar Habaka Cinikinsu Da Sin 

CIIE Ya Ba ‘Yan Kasuwar Afirka Damar Habaka Cinikinsu Da Sin 

November 11, 2025
Me Sabon Tarihin Da Aka Kafa A Baje Kolin CIIE Ke Nunawa?

Me Sabon Tarihin Da Aka Kafa A Baje Kolin CIIE Ke Nunawa?

November 11, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.