Ko meke faruwa? ma’aikata 9,332 da gwamnatin Abba Kabir Yusuf ta dawo da su bakin aiki, sun shiga cikin kunci, inda suka ce, har yau 12 ga watan Disamba, ba su ga albashin watan Nuwamba ba.
Wadannan ma’aikata da ke cikin 12,566 da aka dakatar saboda zargin cewa, ba a bi tsarin daukar ma’aikata da gwamnatin Ganduje ta yi ba, ma’aikatan sun shafe watanni Bakwai suna tsumayin dawo da su bakin aiki.
- Harin Tudun Biri: Tawagar ‘Yan Majalisar Wakilai Na Arewa Ta Bayar Da Gudunmuwar Naira Miliyan N350m
- Dole A Hukunta Wadanda Suka Kai Harin Bom A Kaduna -Majalisar Dattawa
Sanarwar mayar da ma’aikatan bakin aiki ta fito ne daga bakin sakataren gwamnati, Dakta Abdullahi Baffa Bichi, inda ya tabbatar wa jama’a cewa, an ware karin kasafin kudi naira miliyan 507 domin biyan albashin ma’aikatan da aka dawo da su bakin aiki. Amma abun mamaki, ma’aikatan sun ce, su dai har yanzun shiru babu albashi.
Shugaban kungiyar da ke wakiltar ma’aikatan, Abdulrahman Yusuf Adam ya nuna matukar damuwa, inda ya nuna cewa, duk da dawowar su bakin aiki, suna zargin cewa, an cire su daga cikin jadawalin albashin gwamnati.