Akalla ma’aikatan babban bankin Nijeriya 1,500 ne za su koma aiki a ofishinsa na Legas ranar Juma’a bayan da aka yi musu canjin wurin aiki daga hedikwatar, inji rahoton jaridar PUNCH.
Wata majiya a babban bankin ta shaida wa wakilin jaridar cewa, duk da cewa shirin ya samu kalubalen da wasu ‘yan Nijeriya ke ganin cewa, sam bai dace ba, amma bankin ya cigaba da gudanar da shirye-shiryensa, kuma ma’aikatan da abin ya shafa za su ci gaba da aikinsu ranar Juma’a a babban ofishin bankin da ke Legas.
- CBN Ya Nada Sabbin Shugabannin Gudanarwar Wasu Bankuna
- Masana’antun Kauyukan Sin Sun Samu Ci Gaba Yadda Ya Kamata A Shekarar 2023
“Eh, har yanzu ana kan gudanar da shirin, Ma’aikatun da lamarin ya shafa kuma za su ci gaba da aiki a ranar 2 ga Fabrairu, wanda shine makon farko na wata mai zuwa,” in ji majiyar.
Wannan na zuwa ne biyo bayan matakin da sabon shugaban bankin ya dauka na mayar da wasu sassan ma’aikatun CBN zuwa wani sashen bankin da ke Legas domin rage cunkoson ma’aikata a hedikwatar bankin da ke Abuja.