Kwamitin majalisar dattawa mai kula da bin tsari da da’a da sauraron kararrakin jama’a ya ce “sakamakon binciken da ya yi bayan tattaunawa da hukumomin gwamnati ya nuna cewa cin hanci da rashawa ya fi kamari a ma’aikatan gwamnati fiye da sauran sassa.”
A cewar shugaban kwamitin, Sanata Ayo Akinyelure (PDP, Ondo), ma’aikatan gwamnati sun fi ‘yan siyasa cin hanci da rashawa.
Ya bayyana hakan ne a ranar Laraba a Abuja a wajen wani taron bita na kwanaki biyu kan harkokin mulki da sanin ya kamata, da’a da kuma aiwatar da ayyuka akan tsari a ma’aikatun gwamnati da kamfanoni masu zaman kansu a Nijeriya.
Ya ce, in gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari tana son yin nasara a yakin da take yi na yaki da cin hanci da rashawa, dole ne ta fara kawar da cin hanci da rashawa a ma’aikatan gwamnati.
Ya ce, duba da yadda ma’aikatan gwamnati ke shafe shekaru suna hidima wa kasa fiye da ‘yan siyasa “hakan ya kara sa cin hanci da rashawa ke cigaba da wanzuwa a ma’aikatun gwamnati.”