Tawagogin ma’aikatan ceto na kasar Sin na ci gaba da aiki a yankin da ya fi shan wuya na Mandalay da ke tsakiyar kasar Myanmar, sakamakon girgizar kasar da ta afku mai karfin maki 7.9 a makon da ya gabata, inda zuwa yanzu suka ceci mutum takwas da suka tsira daga ibtila’in, da misalin karfe 8 na safiyar ranar Talata, agogon kasar.
A yayin bikin bayar da gudummawar kudi ga wadanda girgizar kasar ta shafa a birnin Nay Pyi Taw a yau Talata, shugaban majalisar gudanarwar kasar Myanmar, Min Aung Hlaing, ya ce, mutanen da suka mutu sakamakon mummunar girgizar kasar wacce ta afku a kasar a ranar Jumma’a, sun kai 2,719, yayin da wasu 4,521 suka jikkata, kana 441 suka bace ba a ji duriyarsu ba har yanzu, kamar yadda kafafen yada labarai na kasar suka ruwaito. (Abdulrazaq Yahuza Jere)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp