Shugaban Kamfanin Man Fetur na Kasa (NNPC), Mele Kyari, ya ce shi da ma’aikatansa ba barayi ba ne, lura da yadda ake cacakar su a kafofin sada zumunta dangane da shigo da gurbataccen mai cikin Nijeriya.
Yayin da ya gurfana a gaban Kwamitin Majalisar Dattawa saboda zargin yin zagon kasa ga bangaren mai, Kyari ya ce a matsayinsa na shugaban NNPC tare da kamfanin sun fuskanci kalaman cin zarafi da kuma bata musu suna daga kafofi da dama.
- Kasar Sin Na Kan Gaba Wajen Neman Ikon Mallakar Fasaha A Fannin Kiyaye Muhalli A DuniyaÂ
- Gwamnan Gombe Ya Bayar Da Umurnin Raba Kayan Abinci Don Rage RaÉ—aÉ—in Kuncin Rayuwa
Kyari ya ce NNPC zai ci gaba da gudanar da ayyukansa kamar yadda doka ta tanada.
A gefe guda kuma ya yi watsi da masu cin mutuncinsu da kuma alkawarin yi wa kasa aiki tukuru.
Takaddama ta kaure tsakanin kamfanin Dangote da NNPC dangane da rashin ba shi danyan mai da kuma zargin kamfaninsa da gabatar da man da ba shi da inganci, abin da ya kai ga mahawara mai zafi a Nijeriya.
Daga bisani shugaban kasa Bola Tinubu ya bai wa NNPC umarnin sayar wa Dangoten mai a farashin Naira.