Gwamnatin Tarayya ta yarda akwai matsaloli na kudi da na aiki a cikin manyan ofisoshin jakadanci da kanana na Nijeriya a kasashen waje, inda ta danganta wannan matsala da karancin kasafin kudi da sauye-sauyen manufofin musayar kudi.
Ma’aikatar Harkokin Wajen ta bayyana haka a ranar Litinin cikin wata sanarwa da mai magana da yawunta, Kimiebi Ebienfa, ya fitar.
- Tinubu Ya Fara Hutun Aiki Na Kwanaki 10 A Faransa Da Birtaniya
- Spence Na Dab Da Kafa Tarihin Zama Musulmi Na Farko Da Zai Buga Wa Ingila Ƙwallo
Ma’aikatar ta amince cewa wadannan matsaloli sun kawo cikas ga tafiyar da ayyukan wasu ofisoshin, wanda ya haifar da jinkirin biyan albashin ma’aikatan gida, kudaden alawus ga jami’an da ke aiki a gida, da kuma biyan haya ga masu gidaje da masu bayar da ayyuka.
“Ma’aikatar ba ta yi shiru ba kan irin takunkumin da iyakace kudi ya sanya a tafiyar da ayyukan ofisoshin, ciki har da rashin iya biyan albashin ma’aikatan gida, biyan bukatun kudi ga masu bayar da ayyuka, haya ga masu gidaje, da kuma alawus ga jami’an da ke aiki a gida,” in ji sanarwar.
Yayin da ta jaddada cewa wannan yanayi na nuna halin tattalin arzikin kasa gaba daya, ma’aikatar ta lura cewa karancin kudi a tsawon shekaru ya ragi ikon ofisoshin wajen gudanar da manyan ayyukan diflomasiyya.
“Dole ne a bayyana, duk da haka, cewa ofisoshin diflomasiyyar Nijeriya ba su da kariya daga halin tattalin arzikin gida da kalubalen da ke tattare da ayyukan gwamnati. Matsalar kudi a ofisoshinmu ta samo asali ne daga iyakokin kasafin kudi a cikin shekaru, wanda ya haifar da karancin rabon kudi,” in ji ma’aikatar.
Sanarwar ta tabbatar wa ‘Yan Nijeriya a gida da kasashen waje cewa kula da walwalar jami’an harkokin kasa da iyalansu na ci gaba da kasancewa babban fifiko ga gwamnatin Shugaba Bola Tinubu.
“Gwamnati na daukar matakai masu karfi da na zahiri don magance batutuwan rabon kudi ga dukkan ofisoshinta a kasashen waje,” in ji ma’aikatar, inda ta bayyana cewa an saki wasu kudade na musamman don rage nauyin da ke kan ofisoshin da abin ya shafa.
Ma’aikatar ta ce, sama da kashi 80 cikin dari na kudaden da ake da su an riga an raba su, inda aka bai wa masu bayar da ayyuka, albashin ma’aikatan gida, da biyan bashin da jami’ai ke da shi fifiko.
Don tabbatar da gaskiya da adalci, an kafa kwamitin tantancewa domin duba bayanan bashi na ofisoshin da kuma tabbatar da cewa biyan kudi ya kasance na gaskiya kuma an raba shi daidai.
Ma’aikatar ta kuma tabbatar da ci gaba da tattaunawa da Ofishin Babban Ma’aikacin Kudi na Tarayya don dawo da ragowar kudaden shekarar kasafin 2024, wanda ta danganta da canje-canjen kimar musayar kudi sakamakon sabbin dokokin manufofin kudi.
“Mun yi imani cewa matsalolin da ake fuskanta yanzu na dan lokaci ne kuma za a shawo kansu ta hanyar kokarin hadin gwiwa na wannan gwamnati. Ma’aikatar Harkokin Wajen ta sake tabbatar da kudurin Nijeriya na diflomasiyyar kasa da kasa mai karfi da tasiri, da kuma kare hakkin da walwalar kowane dan Nijeriya a duniya baki daya,” in ji sanarwar.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp