Jamiin maaikatar harkokin wajen kasar Sin Tong Xuejun ya bayyana yau Jummaa cewa, kasar ta aiwatar da manufofin shiga kasar ba tare da biza ba na bangare daya ga kasashe 29, ciki har da Faransa da Jamus, a wani mataki na kokarin bunkasa tafiye-tafiye na kasa da kasa.
Tong ya kuma bayyana matakan daidaita tsarin neman bizar, inda ya ambaci yadda rage kashi 34 cikin dari na abubuwan da ake bukata a takardar neman bizar ya matukar takaita lokacin da ake bukata wajen kammala aikin takardun.
- Xi: Kasar Sin Za Ta Ci Gaba Da Yin Aiki Tare Da Morocco Wajen Goyawa Muhimman Muradun Juna Baya
- Jawabin Shugaba Xi A Taron G20: Ya Kamata A Bar Adalci Ya Wanzu A Doron Kasa
Jamiin ya kara da cewa, a cikin rubu’i na uku na shekarar 2024, yawan baki ’yan kasashen waje da suka shiga kasar Sin ya kai miliyan 8.19, adadin da ya karu da kashi 48.8 cikin dari idan aka kwatanta da na shekarar da ta gabata. Daga cikin su, miliyan 4.89 sun shigo kasar ne ta tsarin shigowa ba tare da biza ba, wanda ya karu da kashi 78.6 cikin dari bisa makamancin lokacin bara.
Ma’aikatar za kuma ta ci gaba da inganta tsarin shiga kasar ba tare da biza ba, domin saukaka tafiye-tafiye tsakanin kasashe, musamman ga wadanda ke gudanar da harkokin kasuwanci, a cewar Tong. (Yahaya)