Za a gudanar da taron kolin dandalin tattaunawa kan hadin gwiwar Sin da Afirka (FOCAC) na shekarar 2024, daga ranar 4 zuwa 6 ga watan Satumba a nan birnin Beijing. Mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Lin Jian ya gabatar da shirye-shiryen da suka dace na taron kolin a yayin taron manema labarai da aka saba yi a yau Talata 30 ga watan nan.
Jami’in ya bayyana cewa, taron dandalin tattaunawar na bana, shi ne karo na hudu da zai gudana a matsayin taron koli, inda bangarorin Sin da Afirka za su karfafa sada zumunta, da tattauna hadin gwiwa, da ma makomarsu a nan gaba bisa babban jigon “Aiki tare don inganta zamanantar da jama’a, da gina al’umma mai kyakkyawar makoma ta bai daya ga Sin da Afirka”.
- Sin Da Afrika Sun Himmatu Wajen Karfafa Hadin Gwiwar Dijital
- Don Hana Zanga-Zanga, Shugaba Tinubu Ya Amince Da Kafa Ofishin Matasa A Abuja
Jami’in ya kuma bayyana cewa, za a gudanar da taron manyan jami’ai, da taron ministoci na dandalin a ranakun 2 da 3 ga watan Satumba, domin share fagen taron. Kaza lika za a gudanar da jerin wasu harkoki daga ranar 4 zuwa 6 ga watan Satumba, wadanda suka hada da bikin bude taron kolin, da liyafar maraba, da wasannin nuna fasaha, da manyan tarurruka, da babban taron shugabannin kamfanonin Sin da kasashen Afirka, da kuma ganawar da za a shirya tsakanin bangarorin biyu, da dai sauransu.
Jami’in ya bayyana imaninsa cewa, bisa kokarin hadin gwiwa tsakanin Sin da Afirka, taron kolin dandalin tattaunawar hadin gwiwar Sin da Afirka na bana zai samu cikakkiyar nasara, wanda zai shiga sabon mataki na raya dangantakar bangarorin biyu, da kuma rubuta wani sabon babi na gina al’umma mai kyakkyawar makoma ta bai daya ga Sin da Afirka. (Bilkisu Xin)