A yayin ziyarar da ya kai kasashen Afirka a kwanan nan, sakataren harkokin wajen kasar Amurka Antony Blinken, ya sake yin tsokaci kan batun “tarkon bashi na kasar Sin”.
Mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Wang Wenbin, ya musanta wannan batu a yayin taron manema labarai da aka saba shiryawa Alhamis din nan.
Yana mai cewa, batun “tarkon bashi na kasar Sin” karya ce da kasar Amurka da kasashen yammacin duniya suka kirkira, don kaucewa nauyin da ya rataya a wuyansu, wanda ba kowa ne ya yarda da shi ba. Don haka, ya dace su bar gaskiya ta bayyana kanta.
Wang ya ce, bashin da kasashe masu tasowa suka dauki dogon lokaci suna biya, galibi ya shafi masu lamuni na kasuwancin yammacin duniya da kuma cibiyoyi daban-daban.
Bankin duniya ya yi kiyasin cewa, kasashe masu karamin karfi da matsakaita, za su biya bashin dala biliyan 940 a cikin shekaru bakwai masu zuwa. Kuma daga cikin wannan adadi, kaso 67 cikin 100 ana biyansu ne ga masu ba da lamuni na kasuwanci na yammacin duniya da cibiyoyi da dama, Kudaden da ake biyan gwamnatin kasar Sin da cibiyoyin kasuwancin kasar, kashi 14 ne cikin 100 kawai.
Wang ya yi nuni da cewa, kasar Sin ita ce ke kan gaba wajen ba da gudummawa ga ci gaba da aiwatar da shirin rage basussuka na kungiyar G20.
Sabanin haka, masu ba da lamuni na kasuwanci na yammacin duniya da cibiyoyi daban-daban, sun ki shiga ayyukan yafe basussuka, bisa la’akari da kare martabar lamunin da suka bayar, kuma ba su ba da gudummawar kwatankwacin na kasar Sin ba don sassauta nauyin bashin dake kan kasashe masu tasowa.(Ibrahim)