Mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Mao Ning, ta bayyana a yau Jumma’a 5 ga wata cewa, ya dace kasar Amurka ta zama mai hangen-nesa da kara nuna hakuri, a yayin da take kallon hadin-gwiwar dake tsakanin kasar Sin da kasashen Afirka, kana, al’ummar Afirka ne ya fi dacewa su yi tsokaci, kan hadin-gwiwar su da kasar Sin.
Wasu rahotanni sun ce rukunin Afirka, na kwamitin kula da harkokin waje na majalisar wakilan Amurka ya kira wani taro kwanan nan, inda ya nuna damuwa kan hadarin dake tattare da biyan basussuka, sakamakon wasu ayyukan da suka shafi tattalin arzikin da kasar Sin ta gudanar a nahiyar Afirka, kana a cewar sa, kasar Sin ta boye wasu abubuwa a hadin-gwiwar ta da Afirka.
Game da wannan batu, Mao Ning ta ce, kasar ta ta dade tana tsayawa kan manufar bude kofar ta ga kasashen waje ba tare da wata rufa-rufa ba, da aiwatar da hadin-gwiwa tare da bangaren Afirka daidai da bukatunta, da habaka fannonin hadin-gwiwar, har ma kwalliya ta riga ta biya kudin sabulu.
Mao ta kara da cewa, cibiyoyin hada-hadar kudi na kasa da kasa, da sauran masu bada lamuni na kasa da kasa su ne ke kan gaba wajen samar da rance ga kasashen Afirka. Hakika, manufar Amurka ta kara kudin ruwa fiye da kima, ta sa kasashen Afirka suna kara kashe kudade wajen biyan basussuka, al’amarin da ya zama wani muhimmin dalili da ya janyo matsalar biyan bashin da kasahen Afirka ke fuskanta. (Murtala Zhang)