Mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin, Wang Wenbin ya amsa tambayar da aka yi masa a yau Alhamis, game da kalaman sakataren harkokin wajen Amurka Antony Blinken da suka shafi Taiwan, inda Wang ya jaddada cewa, Taiwan, yanki ne da ba za’a iya ware shi daga kasar Sin ba, kana, daidaita batun Taiwan, harkokin cikin gida ne na kasar, wanda al’ummar kasar kadai ke da ikon yanke shawara a kai.
Antony Blinken ya bayyana cewa, kasar Sin za ta iya fatattakar Taiwan kafin shekara ta 2027. Game da wannan kalami na jami’in Amurka, Wang ya ce, kasar Sin za ta yi iya kokarinta don tabbatar da dunkulewar dukkanin sassan kasa baki daya ta hanyar lumana, amma ba ta yi alkawarin yin fatali da karfin soja ba, wato za ta dauki duk wani matakin da ya wajaba in akwai bukata, kan wadanda suka tsoma baki, gami da ‘yan tsirarrun da suke yunkurin balle Taiwan daga kasar Sin.
Game da batun da ya jibanci bankin Silicon Valley na Amurka, Wang ya ce, kasarsa ta bukaci Amurka, da ta aiwatar da manufofin kudi ta hanyar da ta dace, don tabbatar da hasashen kasuwanni, da farfado da imanin masu zuba jari, maimakon ta dauki matakan da ka iya haifar da mummunan tasiri, kamar babbar matsalar kudi da ta wakana a shekara ta 2008. (Murtala Zhang)