Mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin, Wang Wenbin ya maida martani, dangane da zargin da wasu manyan jami’an gwamnatin Amurka, da na bankin duniya suka yiwa kasar Sin, inda ya bayyana cewa, kasar Sin ba ita ce tushen saka wa kasashen Afirka “tarkon bashi” ba, akasin haka, aminiya ce dake kokarin taimakawa kasashe masu tasowa, ciki har da na Afirka, don su fidda kansu daga cikin irin wannan tarko na talauci.
Jami’in ya kara da cewa, wasu ‘yan siyasar kasashen yammacin duniya na yunkurin kitsa karairayi daban-daban, da zummar illata hadin-gwiwar Sin da kasashe masu tasowa. Wang ya yi misali daga cikin rahoton bankin duniya, mai cewa daga cikin dukkan bashin da aka baiwa kasashen Afirka, yawan bashin da hukumomin kudi dake kunshe da bangarori daban-daban, wanda ‘yan kasuwan bayar da bashi suka bayar, ya kai kusan kaso 75 bisa dari, abun dake nuna cewa, su ne ginshikan samar da bashi ga kasashen Afirka. Kana, bashin da bankin duniya, da asusun bada lamuni na duniya wato IMF suka samar, ya kai kusan kaso 70 bisa dari, cikin bashin da hukumomin kudi dake kunshe da bangarori daban-daban suka samar.
Ya ce Amurka, babbar kasa ce ta farko da take da hannun jari a bankin duniya da IMF, kuma kasar Amurka da kasashen Turai, su ne manyan kasashen dake samar da bashi ga kasashen Afirka. A sabili da haka, ya zama dole su dauki nauyin taimakawa kasashen Afirka, wajen warware matsalar bashin da suke fuskanta. (Murtala Zhang)