Ministan harkokin wajen Sin Wang Yi, ya karbi bakuncin liyafar sabuwar shekara ta ma’aikatarsa, jiya Jumma’a a cibiyar gabatar da wasannin fasahohi ta Beijing.
Wang Yi ya bayyana cewa, harkokin wajen Sin sun daukaka burin gina al’umma mai makoma ta bai daya ga bil adama, da ingiza zaman lafiya da sauke nauyin da ya dace domin samun ci gaba. Ya kuma jaddada cewa, harkokin diplomasiyya na kasar Sin, sun bayar da gagarumar gudunmowa ga karin zaman lafiya da kuzari ga duniya mara tabbas.
- An Saki Shugaban Hukumar Yaƙi Da Cin Hanci Ta Kano
- AC Milan Ta Kammala Ɗaukar Kyle Walker Daga Manchester City A Matsayin Aro
A cewarsa, kasar Sin ta shirya aiki da dukkan kasashe wajen bayar da fifiko ga zaman lafiyar duniya da shawo kan rikice-rikice da rarrabuwar kawuna da inganta abota da hadin gwiwa. Yana mai cewa “mu hada hannu tare, mu inganta fahimtar juna tsakanin mabambantan al’adu da gina al’umma mai makoma ta bai daya ga bil adama.”
A nasa bangare, jakadan Kamaru a kasar Sin, kuma shugaban kungiyar jami’an diplomasiyya dake Sin, Martin Mpana, ya yi wa al’ummar Sinawa fatan alheri a sabuwar shekara, a madadin kungiyar. Ya kuma yabawa manufar diplomasiyyar kasar Sin, bisa yadda take sauke nauyin dake wuyanta a matsayinta na babbar kasa, kuma mai bayar da gudunmowa ga warware matsalolin rashin tabbas da kalubalen duniya. Ya kara da cewa, kasa da kasa na son zurfafa abota da karfafa musaya da inganta hadin gwiwa da Sin, domin gina al’umma mai makoma ta bai daya ga bil adama.
Liyafar ta samu halartar Yin Li, mamban ofishin siyasa na kwamitin kolin JKS kuma sakataren kwamitin jam’iyyar na birnin Beijing, da jami’an diplomasiyya daga kasashe daban-daban da wakilan hukumomin kasa da kasa dake Sin da jami’ai daga sassan gwamnatin kasar Sin. An yi kiyasin mutane kimanin 400 ne suka halarci liyafar. (Fa’iza Mustapha)