Ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin ta bayyana yanayin tattaunawar da aka yi ta wayar tarho tsakanin shugaban kasar Sin Xi Jinping da takwaransa na Amurka Donald Trump, a matsayin mai kyau da ma’ana kuma ta abota.
Kakakin ma’aikatar Mao Ning, ta tabbatar yayin taron manema labarai na yau Talata cewa, Amurka ce ta nemi a yi tattaunawar. Ta kara da cewa, tun farkon wa’adin mulki na biyu na shugaba Trump, shugabannin biyu ke tuntubar juna a kai a kai.
Mao Ning ta kara da cewa, shugabannin biyu sun yi musayar ra’ayi kan batutuwan da ke jan hankalinsu, tare da nanata cewa, tuntubar juna na da muhimmanci ga raya dangantakar Sin da Amurka ta hanyar da ta dace. (FMM)














