Ma’aikatar kananan hukumomi da masarautu ta Jihar Zamfara ta gabatar da bitar kasafin kudi na shekara ta 2025 ga majalisar kananan hukumomi 14 da ke cikin jihar.
Kwamishinan ma’aikatar kananan hukumomi da masarautu, Hon Ahmad Yandi shi ne ya jagoranci bitar, ya bayyana cewa, sun kira wannan bitar ne don tsaftace kasafin kudin kuwace karamar hukuma da gyare gyaren da ya kamata a yi kafin zuwa jamalisar dokokin jihar.
- Yadda Turmutsutsin Rabon Kayan Abinci Ya Dagula Karsashin Kirsimeti
- Yadda Turmutsutsin Rabon Kayan Abinci Ya Dagula Karsashin Kirsimeti
A cewarsa, a wannan karon kasafin kudin za a sanya gyaran gidajan sarakuna da hakimai uku a kowace karamar hukuma, domin su ne iyayan al’umma.
Kwamishinan ya kara da cewa kowane kansila ya duba ayyukan da ya ba da wanda aka sa a kasafin kudin domin al’ummasa su amfana da wakilincinsa.
Shi ma a nasa jawabin, mukadashin Babban Sakataren Ma’aikatar, Dakta Ibrahim Lawal Maishanu, ya bayyana cewa, kasafin kudi na kananan hukumomi shi ne ke tantance ayyukan da kowace karamar hukuma za ta yi a shekarar 2025, domin haka dole ne a tsaya a ga yadda kasafin kudin aka tsarashi bisa doka da oda.
Daraktan tsare-tsare, Murtala Yusuf ya bayyana cewa, tun daga gwamanatin tarayya har zuwa jihohi da kananan hukumomi ana auna kasafin kudin ne a kan yadda farashin gangar danyan mai da kuma hanyoyin samun kudin shiga ake tsara shi, wannan bitar zai haska dukkan ayyukan kowace karamar hukumar da kudaden ayyukanta.
Daraktan ayyuka na ma’aikatan, Surajo Muhammad ya tantance ingancin ayyukan ma’aikatar kananan hukumomi.
Shugaban karamar hukumar Talata Mafara, Hon Yahaya Yari ya tabbatar da cewa, kudirin gwamna na samar da tsaro shi ne suka fi bai wa fifiko, domin babu abun da zai samu na ci gaba ba tare da zaman lafiya ba.
Shugaban kungiyar ALGON, kuma shugaban karamar hukumar Zurmi, Hon Samaila Hussaini Moriki ya tabbatar da cewa, kananan hukumomi za su yi iya bakin kokarinsu wajen samar da kasafin kudi mai tsafta da zai taimaki wa al’umma.