Ma’aikatar kasuwanci ta kasar Sin ta yi kira ga bangaren Amurka, da ya gaggauta gyara kurakurai, ya kuma shiga tattaunawar cinikayya da sahihiyar zuciya, kana ya yi aiki tare da bangaren Sin don cimma matsaya guda.
Kakakin ma’aikatar ne ya yi kiran yayin da yake tsokaci, dangane da zargin da Amurka ta yi, cewa Sin ta dage tattaunawa ta wayar tarho da aka tsara yi, domin tattauna matakan Sin din masu nasaba da tantance batun fitar da albarkatun farin karfe ko “rare earth”, da ma shawarar da Amurka ta gabatar, cewa kamata ya yi sassan biyu su lalubo hanyar maido da daidaiton alaka tsakaninsu.
Kakakin ya ce Sin ta riga ta sanar da matsayarta ga bangaren Amurka, karkashin tsarin tattaunawa kan batun ciniki tsakanin kasashen biyu, kafin ma ta sanar da matakan tantance batun fitar da albarkatun na farin karfe, kuma sassan biyu suna tuntubar juna karkashin dandalinsu na tattauna batutuwan tattalin arziki da cinikayya, kuma a ranar Litinin din farkon makon nan ma bangarorin biyu sun zanta da juna.
Daga nan sai kakakin ya ce, “Ba zai yiwu bangaren Amurka ya nemi tattaunawa a bangare guda, alhali a daya hannun yana barazanar kaddamar da sabbin takunkumai kan kasar Sin ba. Wannan ba ita ce hanya mai dacewa ta gudanar da cudanya da Sin ba.” (Saminu Alhassan)