A jiya Juma’a ne mai magana da yawun ma’aikatar tsaron jama’a ta kasar Sin ya bayyana rashin amincewa da barazanar da Amurka ta yi ta sanya karin harajin kashi 10 cikin dari kan kayayyakin da kasar Sin ke fitarwa. Ya bayyana hakan ne yayin da yake mayar da martani ga wata tambayar manema labarai kan barazanar karin haraji da Amurka ta yi, wanda zai fara aiki daga ranar 4 ga Maris, kuma ta ambaci matsalar fentanyl a matsayin dalilin.
Kakakin ya ce, kasar Sin ta ba da goyon baya ga Amurka wajen tinkarar matsalar fentanyl bisa dalilan jin kai, kuma ta samu sakamako mai kyau. Ya kara da cewa, rikicin fentanyl matsala ce da tushenta ke cikin Amurka. Yana mai cewa, bangaren Amurka ya yi watsi da hakikanin gaskiya kuma ya kasa magance ainihin batutuwan da suka shafi bukatun miyagun kwayoyi yayin da yake dora laifin kan wasu kasashe. Abin da Amurka take yi ba zai taimaka wajen magance matsalar ba, kuma zai yi illa sosai ga hadin gwiwar Sin da Amurka kan yaki da muggan kwayoyi. (Mohammed Yahaya)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp