Mai magana da yawun ma’aikatar tsaron kasar Sin, Wu Qian ya bayyana cewa, kamata ya yi a samar da ka’idoji da sassan da ba za a iya tsallakawa ba game da tattaunawa tsakanin sojojin Sin da Amurka.
Wu Qian ya bayyana hakan ne, yayin da yake karin haske, kan wani bincike da kafofin watsa labarai suka gabatar, inda ya nuna damuwarsa kan yadda alaka da ma musaya tsakanin sojojin Sin da Amurka ke neman gamuwa da cikas.
Wu ya ce, alakar sassan tana nan, haka kuma bangarorin biyu na ci gaba da gudanar da tattaunawar sahihan bayanai masu inganci ta hanyoyin diflomasiya na soja.
Sai dai Wu ya ce, duk da haka, hakika akwai matsaloli da cikas da dama a cikin dangantakar. Yana mai cewa, galibin irin wadannan matsaloli da cikas, bangaren Amurka ne ke haddasa su.
Wu ya ce, yayin da bangaren Amurka ke yin zagon kasa ga moriyar kasar Sin, bai kamata a yi tunanin cewa, sojojin kasar Sin za su yi magana kamar babu abin da ya faru.
Don haka ya ce, ya kamata bangaren Amurka ya nuna sahihanci da kuma daukar kwararan matakai, don samar da yanayin dawo da dangantakar kasasahen dake da nisa a tsakaninsu kan turba mai kyau. (Ibrahim Yaya)