Yau Laraba, kakakin ma’aikatar harkokin wajen Sin Guo Jiakun ya gudanar da taron manema labarai da aka saba.
Game da batun da Amurka ta nuna cewa za ta sa wa kamfanonin Sin da abin ya shafa takunkumi bisa zargin wai “an tilasta wa mutane yin aikin dole”, Guo Jiakun ya ce, abin da suke fada kan haka gaba daya karya ne. Inda ya ce, matakin da Amurka ta dauka nufinsa kawai shi ne tsoma baki cikin harkokin cikin gida na Sin, da gurgunta moriyar Sin, da kuma dakile ci gaban Sin. Ya kuma jaddada cewa, kasar Sin za ta dauki kwararan matakai don kiyaye hakki da muradun kamfanoninta.
- Abubuwan Dake Kunshe Cikin Rahoton Shekara-Shekara Game Da Cinikin Shige Da Fice Na Kasar Sin
- ‘Yan Bindiga Sun Koma Neja Bayan Sulhu Da Gwamnatin Kaduna
Har ila yau, a kan matakin Amurka na kayyade shigowar motoci masu amfani da lantarki da Sin ta kera bisa dalilin “kiyaye tsaron kasa” kuwa, Guo Jiakun ya bayyana cewa, Sin tana nan a kan bakanta na cewa Amurka ta daina gamin-gambiza a kan manufar tsaron kasa, tare da dakatar da yaki mara dalili da kamfanonin kasar Sin.
A game da dangantakar tattalin arziki da cinikayya tsakanin Sin da kasashen Turai kuwa, Guo Jiakun ya bayyana cewa, ana fatan bangarorin Turai da Sin su yi kokari tare, da bin ka’idojin kasuwanci mai kofa a bude, da yin takara cikin adalci, ta yadda dangantakar tattalin arziki da cinikayya a tsakaninsu za ta bunkasa lami lafiya.(Safiyah Ma)