Ma’aikatar yada labarai ta Jihar Kaduna ta kulla wata yarjejeniyar hadin gwiwa da Hukumar Kididdiga ta Jihar (BoS) domin shirya horo na musamman ga ’yan jarida akan yadda zasu rika bayar da sahihan rahotannin da bayanan kididdiga.
Manufar wannan shiri ita ce, cike giɓi tsakanin bayanan gwamnati masu rikitarwa da fahimtar jama’a, domin inganta gaskiya, daukar nauyi da kuma karfafa hulda tsakanin al’umma da harkokin mulki.
- 2027: Ko Kano Ta Zauna Lafiya Ko Ta Hautsine, Sai Mun Sauke Gwamna Abba — Shugaban APC
- Zulum Ya Raba Motocin Sintiri 63 Ga Hukumomin Tsaro A Borno
An kaddamar da wannan hadin gwiwar ne a ranar Talata lokacin da Babban Jami’in Kididdiga na Jiha, Dakta Bukar Baba Alhaji, ya kai ziyarar ban girma ga Kwamishinan yada labarai Malam Ahmed Maiyaki, a offishinsa.
Dakta Bukar ya bayyana wannan hadin gwiwar a matsayin abu mai muhimmanci wanda yazo a kan gaba wajen karfafa wayar da kan jama’a game da rawar da sahihan bayanai suke takawa wajen tsara ci gaba da samar da manufofi masu tushe , da dorewar cigaban kasa.
Dakta Bukar, ya jaddada muhimmancin hadin gwiwa da kafafen yada labarai wajen isar da bayanan Hukumar ga al’umma.
A cikin jawabinsa, Kwamishinan yada labarai Malam Ahmed Maiyaki, ya yaba da wannan shiri tare da tabbatar da cikakken goyon bayan Ma’aikatarsa ga manufofin Hukumar.
Yace samar da sahihan da kafa gwamnati mai wacce da dogara da adalci yana daga cikin manifofi da kudirorin gwamnatin jihar Kaduna wanda hakan zai taiama wajen kawo ci gaba ga al’umma baki daya.












