Bayanai na baya-bayan nan da hukumar kula da harkokin musayar kudaden waje ta kasar Sin ta fitar sun nuna cewa, ya zuwa karshen watan Afrilu, asusun ajiyar kudaden waje na kasar Sin ya kai dalar Amurka biliyan 3281.7, wanda ya karu da dalar Amurka biliyan 41 ko kashi 1.27 bisa dari daga karshen watan Mayu. Kazalika, ma’aunin asusun ajiyar kudaden waje na kasar Sin ya kasance cikin daidaito da sama da dalar Amurka tiriliyan 3.2 na tsawon watanni 17 a jere.
Wani jami’in hukumar musayar kudaden waje ta kasar Sin ya bayyana cewa, tattalin arzikin kasar Sin yana cikin kyakkyawan yanayi, tare da nuna juriya da karfi a ci gaban tattalin arziki, wanda hakan zai taimaka wajen tabbatar da kwanciyar hankali a ma’aunin asusun ajiyar kudaden waje. (Mai fassara: Mohammed Yahaya)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp