Mambobin ƙungiyar ƴan uwa Musulmi a Nijeriya (IMN), da aka fi sani da Shi’a, sun gudanar da zanga-zanga a garin Kano yau Asabar don nuna adawa da maganganun shugaban Amurka, Donald Trump, wanda ya yi barazanar mamaya ga Nijeriya don yaƙar ƴan ta’adda.
Masu zanga-zangar, waɗanda suka riƙa tattaki a manyan titunan birnin Kano, sun riƙe tutoci da saƙonnin ƙaryata iƙirarin Trump cewa ana kisan kiyashi ga Kiristoci a Nijeriya. Wasu daga cikinsu an gan su suna jan tuta ta Amurka a ƙasa, yayin da wasu suka ɗauki hoton Trump suna nuna rashin amincewa da maganganunsa.
- Batun Kawo Harin Soja: ‘Yan Nijeriya Sun Yi Watsi Da Barazanar Trump
- NUJ Ta Yi Maraba Da Sakin Ƴan Jaridar Da DSS Ta Kama A Jana’izar Mahaifiyar Shugaban APC
Trump ya bayyana cewa Nijeriya ta zama ƙasa mai matsala ta musamman, yana zargin cewa ana zaluntar Kiristoci, tare da yin barazanar tura Sojojin Amurka idan gwamnati ta kasa dakatar da hakan. Haka kuma, ya umarci Ma’aikatar yaƙin Amurka da ta fara shirin kai farmaki idan buƙatar hakan ta taso.
Sai dai a martanin da ƙungiyar IMN ta fitar ta hannun Abdullahi Danladi na sashin albarkatun ƙungiyar, ta bayyana kalaman Trump a matsayin na tayar da fitina da ƙarya, tana zargin ƙasashen yamma da ƙoƙarin haifar da rarrabuwar kawuna a tsakanin Musulmai da Kiristoci a Nijeriya. Danladi ya ce matsalolin ƙasar ba na addini ba ne, illa dai sakamakon cin hanci da rashawa, da son kai na ’yan siyasa.
Ya jaddada cewa ƙungiyar IMN tana goyon bayan zaman lafiya da haɗin kai tsakanin al’ummomi, tare da kira ga ’yan Nijeriya da su guji faɗawa cikin tarkon siyasar ƙasashen waje da ke neman raba kan al’umma.














