Netumbo Nandi-Ndaitwah, mai shekaru 72, ta zama mace ta farko da ta zama shugabar kasa a Namibia, bayan jam’iyyar SWAPO ta lashe zaben shugaban kasa.
Nandi-Ndaitwah, ita ce mataimakiyar shugaban kasa ta yanzu.
- An Gudanar Da Taron Gabatar Da Tashar Jiragen Ruwa Ta Ciniki Cikin ‘Yanci Ta Hainan
- Sin Ta Jaddada Kudurinta Na Kara Inganta Daidaito Da Tsaro A Tekun Guinea
Ta samu kashi 57 na kuri’un da aka kada, wanda ya wuce kashi 50 da ake bukata don lashe zabe.
Wannan nasara ta kara wa jam’iyyar SWAPO tsawon shekaru 34 tana mulki tun bayan samun ‘yancin kai daga hannun Afirka ta Kudu a 1990.
Babban abokin hamayyarta, Panduleni Itula na jam’iyyar IPC, ya samu kashi 26 na kuri’un da aka kada.
Wannan nasara ta Nandi-Ndaitwah ta kafa tarihi a siyasar kasar.