Mojisola Lasbat Meranda ta kafa tarihin zama mace ta farko da aka zaɓa a matsayin shugabar majalisar dokokin Jihar Legas.
An zaɓi Meranda ne bayan da aka tsige tsohon shugaban majalisar, Mudashiru Obasa, a wani zaman majalisar da aka yi ranar Litinin.
- Huldar Sin Da Afirka Za Ta Zama Abin Koyi Wajen Gina Al’umma Mai Makomar Bai Daya Ta Daukacin Bil’adama
- Cinikayyar Waje Ta Kasar Sin Ta Kai Sabon Matsayi A Shekarar 2024
Meranda mai shekara 44, tana wakiltar mazaɓar Apapa 1 a majalisar, kuma kafin yanzu, ita ce mataimakiyar shugaban majalisar da aka tsige.
An rantsar da ita a zauren majalisar dokokin jihar, inda ta yi alƙawarin yin aiki bisa gaskiya da doka.
“Na ɗauki alƙawarin cewa zan yi gaskiya da riƙon amana a matsayina na shugabar majalisar dokokin Jihar Legas, bisa tanadin kundin tsarin mulkin Nijeriya,” in ji Meranda a lokacin rantsar da ita.
Tun da aka kafa majalisar dokokin Jihar Legas, wannan shi ne karo na farko da aka zaɓi mace a matsayin shugaba, a tarihin majalisar dokokin jihar.