• English
  • Business News
Tuesday, October 28, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Madarar Shanu Da Nijeriya Ke Samarwa Ta Karu Da Tan Miliyan 1.4 A Shekara Biyar

by Abubakar Abba
4 months ago
Nijeriya

Gwamnatin tarayya ta sanar da cewa, Nijeriya ta kai wani mataki a duniya a bangaren samar da wadatacciyar Madarar Shanu.

Burin kasar a yanzu shi ne, samar da Madara ta kimanin dala biliyan 1.5, wacce kuma za a rika fitar da ita zuwa kasashen ketare a duk shekara tare da kuma da samar da wadda ake bukata a cikin kasar, wadda yawanta ya kai kimanin tan 1.5, (Lita biliyan 1.5) a duk shekara.

  • Har Yanzu Da Akwai Jihohin Da Malaman Makaranta Ke Karbar Albashin Naira 18,000
  • Abba Ya Dace Ya Zama Gwamnan Kano Na Har Abada Ba Shekaru 8 Kaɗai Ba – Arch Ali Hassan

A halin yanzu, kasar na samar da akalla tan 700,000 na madara a duk shekara, idan aka kwatanta da tan miliyan 1.6 da ake amfani da ita, inda a duk shekara ake kashe sama da dala biliyan 1.5 wajen shigo da madarar; wanda hakan ya kai saura kashi  60 cikin 100.

Ministan Ma’aikatar Bunkasa Kiwon Dabbobi, Alhaji Idi Mukhtar Maiha, a jawabinsa ranar bikin madarar Shanu ta duniya da aka gudanar a kwanakin baya a Abuja ya bayyana cewa, akwai bukatar a cike gibin da ake da shi na samar da madarar nan da shekaru biyar masu zuwa.

“Nijeriya ba wai kawai ta na da burin kamo duniya wajen samar da madarar ba ne, amma tana da burin kasancewa kan gaba wajen samar da madarar,“ in ji Mukhtar.

LABARAI MASU NASABA

Sharhi Kan Noman Agwaluma A Nijeriya

Gwamnatin Jihar Taraba Ta Ayyana Yi Wa Kasuwannin Sayar Da Dabbobi 9 Garanbawul

“Abin da muke son cimma shi ne, a duk shekara mu tabbatar da ganin mun rubanya yawan madarar da ake samarwa kasar a kasar daga tan miliyan 700,000 zuwa tan miliyan 1.4 daga nan zuwa shekara biyar masu zuwa”, a cewar Ministan.

“A Nijeriya akwai sama da Shanu miliyan 20.9, Tumaki sama da miliyan 60, Awakai sama da miliyan 1.4”, in ji shi.

Kazalika, Minstan ya kara da cewa; burin shi ne ganin an kara bunkasa tattalin arzikin kasar tare da kuma kara samar da ayyukan yi ga ‘yan kasar.

“Ina son fayyace cewa, ba wai batu ne kawai na yawan Shanun da ake da su a kasar nan ba, batu ne na jama’a da samar da ayyukan yi, habaka kasuwanci da kuma kara daga kimar tattalin arzikin kasar da kuma samar da madarar da za ta gina jikin yara kanana”, a cewar tasa.

Ministan ya ci gaba da cewa, wannan batu ne na matasan kasar da suke da burin fara yin sana’ar sarrafa madarar Yagot.

Ya kara da cewa, tuni gwamnatin tarayya cikin watanni biyu da suka gabata ta hanyar yin amfani da cibiyar gudanar da bincike ta kiwon dabbobi da ke garin Zariya a Jihar Kaduna, ta fara yin rijistar wasu nau’ika takwas na ciyawar da ake ciyar da dabbobi, wanda wannan aiki shi ne karo na farko a cikin shekaru 48 da suka wuce a fadin kasar nan.

Ministan ya bukaci daukacin matasan kasar nan, da su yi amfani da fasahar da suke da ita da kuma samar da dabaru, musamman domin kara ciyar da fannin na samar da madarar Shanun a wannan kasa.

“Muna da bukatar samar da wata kafar sadarwa da za ta rika sada masu sarrafa madara a kasar, musamman domin kara samar musu da kasuwa da kuma masu bayar da daukin kudade a fannin na samar da madara,” a cewar Ministan.

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Sharhi Kan Noman Agwaluma A Nijeriya
Noma Da Kiwo

Sharhi Kan Noman Agwaluma A Nijeriya

October 18, 2025
‘Yansanda Sun Cafke Ɓarayi 13 Tare Da Ƙwato Shanu 27 A Kaduna
Noma Da Kiwo

Gwamnatin Jihar Taraba Ta Ayyana Yi Wa Kasuwannin Sayar Da Dabbobi 9 Garanbawul

October 18, 2025
Dalilin Bankin AfDB Na Yin Hadaka Da WFP Da IFPRI
Noma Da Kiwo

Dalilin Bankin AfDB Na Yin Hadaka Da WFP Da IFPRI

October 18, 2025
Next Post
Jirgin Alhazai Na Farko Ya Iso Jihar Jigawa

Jirgin Alhazai Na Farko Ya Iso Jihar Jigawa

LABARAI MASU NASABA

JIBWIS Ta Miƙa Takardar Koke Ga Gwamnatin Kaduna Kan Zargin Wasu Malamai Da Yunƙurin Tada Husuma

JIBWIS Ta Miƙa Takardar Koke Ga Gwamnatin Kaduna Kan Zargin Wasu Malamai Da Yunƙurin Tada Husuma

October 28, 2025
An Gudanar Da Taron Musamman Na Tattaunawa Tsakanin Sassan Kasa Da Kasa A Afrika Da Kudu

An Gudanar Da Taron Musamman Na Tattaunawa Tsakanin Sassan Kasa Da Kasa A Afrika Da Kudu

October 28, 2025
Zamfara Ta Fara Sauyawa Zuwa Jihar Fasahar Zamani, In ji Gwamna Lawal

Zamfara Ta Fara Sauyawa Zuwa Jihar Fasahar Zamani, In ji Gwamna Lawal

October 28, 2025
Masanan Kasar Sin Da Afirka Sun Hada Karfi Da Karfe Don Habaka Samun Wadatar Abinci Da Zamanantar Da Aikin Gona

Masanan Kasar Sin Da Afirka Sun Hada Karfi Da Karfe Don Habaka Samun Wadatar Abinci Da Zamanantar Da Aikin Gona

October 28, 2025
Rikicin Manoma Da Makiyaya Ya Yi Ajali Tare Da Jikkata Wasu A Gombe

Rikicin Manoma Da Makiyaya Ya Yi Ajali Tare Da Jikkata Wasu A Gombe

October 28, 2025
Kuri’un Jin Ra’ayin Jama’a Na CGTN Sun Nuna Gamsuwar Jama’a Ga Tsarin Jagoranci Na Sin

Kuri’un Jin Ra’ayin Jama’a Na CGTN Sun Nuna Gamsuwar Jama’a Ga Tsarin Jagoranci Na Sin

October 28, 2025
Kano Ta Bai Wa Mata 5,200 Tallafin Naira Miliyan 260

Kano Ta Bai Wa Mata 5,200 Tallafin Naira Miliyan 260

October 28, 2025
An Kusa Kammala Shirye-shiryen Baje Kolin CIIE Karo Na Takwas

An Kusa Kammala Shirye-shiryen Baje Kolin CIIE Karo Na Takwas

October 28, 2025
Gwamna Bago Ya Amince Da Biyan Karin Albashin Naira 20,000 Ga Ma’aikata 

Gwamnatin Neja Ta Bayar Da Hutun Kwanaki 2 Don Zaɓen Ƙananan Hukumomi

October 28, 2025
Fasahohin Sin Za Su Iya Kyautata Makomar Nahiyar Afrika

Fasahohin Sin Za Su Iya Kyautata Makomar Nahiyar Afrika

October 28, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.