Yawan magidanta masu samun mafi karancin kudin shiga a Amurka ya kai miliyan 11.5. Tun daga shekarar 2009, ma’aunin kudin shiga mai tushe a awa daya da gwamnatin kasar ta kayyade bai canja ba, lamarin da ya sa darajar kudin dala na Amurka 1 a shekarar 2023 ya ragu da kashi 70% bisa na wannan shekara. Wadannan magidanta ba su da isashen kudin shiga na biyan abinci, da kudin hayar gidaje, da sayen makamashi da sauransu.
Rashin daidaituwar rarraba kudin shiga da Amurka ke fuskanta ya dade yana adabar mutanen kasar, kuma hakan na haifar da rashin kudin shiga ga masu aiki, da kuma rashin karfin tsarin ba da tabbaci ga tattalin arziki, da zamantakewar al’umma, lamarin da ya haddasa gibin matalauta da masu wadata mafi tsanani tun bayan barkewar rikicin tattalin arzikin kasar a shekarar 1929. A cikin watannin Yuli, da Agusta, da Satumban bara, kashi 66.6% na dukkan dukiyoyin al’ummar Amurka na hannun mutane da yawansu bai wuce kashi 10% kacal cikin al’ummar kasar ba, yayin da jama’ar kasar da yawansu ya kai kashi 50% suna mallakar dukiyoyin da ba su wuce kashi 2.6% kacal ba.
Shirin jin ra’ayin jama’a mai lakabin “Gallup” na kasar ya sanar da cewa, daga watan Janairu zuwa Disamba a shekarar 2023, jama’ar Amurka kashi 76% zuwa 80%, sun nuna rashin jin dadi da yanayin bunkasuwar kasar, kana kashi 76% na ganin cewa, suna bin hanyar kuskure. Da ganin wadannan sahihan alkaluma, muna iya gane cewa, “mafarkin Amurka ”, wanda ‘yan siyasar kasar ke yunkurin cusawa cikin zukatan Amurkawa ya rube, sakamakon tsarin siyasa irin na kudade, da takara ba tare da adalci ba a tsakanin jam’iyyu daban-daban na kasar. (Mai zane da rubutu: MINA)