Ci gaban tattaunawa da jarumar Kannywood AMINA HARUNA ABDULLAHI wadda aka fi sani da AMINA MILONIYA, inda a wannan makon ta yi bayani a kan fahimtar fim a tsakanin mutane da kuma wata magana da ta ce tana ba ta tsoro game da harkar fim har ma ayyana cewa yanzu burinta bai wuce gobe-gobe ta samu mijin aure ta yi ba. Ga dai tattaunawar tare da RABI’AT SIDI BALA kamar haka;
Me ya sa ki ke son taka rawar ta masifa, kikan taba masifar ne a gida ko kuwa kawai burge ki ya ke yi?
Kawai ina so ne, saboda yana burge ni sosai gaskiya, kuma a lokacin ina jin na shiga cikin aikin sosai, in aka ban aikin na fito a mai masifa sai ki ga har kari nake yi. In aka ce min ga aikina da ya danganci masifa sai ki ga ina jin har kari nake yi. Amma tsakani da Allah ban da masifa a gida (Dariya) kawai dai ina so, a unguwa ba ni da abokin fada haka ma cikin gida, kawai yana yi min dadi ne.
Da wadanne jarumai aka fara hada ki a fim?
Kamar fim din da na fara fitowa, jarumin da na fara aiki da shi ne Al’amin Buhari, shi ne ya fito a mijina ni kuma na hadu da cuta ta shanyewar jiki.
Da wanne Jarumi ko Jaruma ki ka fi so a hada ki a fim?
Gaskiya kowanne jarumi aka hada ni fim da shi muna yin aiki ba tare da an samu matsala ba, duk jarumin da aka hada ni da shi ina aiki da shi, kuma ba ma samun wata matsala, kamar irin su; Tanimu Akawu, Al’amin Buhari, Alhaji Dan Asabe Olala, dukkansu dai da sauransu gaskiya na yi fim da su, kuma ban samu wata matsala ba. sannan cikinsu ma duk wanda ya ke da aiki yana kira na na zo wajen aikin, kin ga kamar bai fi sati biyu ba, Ali Jita ya zo yin waka ana neman uwa sun kira ni irin haka, “Aunty Amina zo ga aikinki” da sauransu.
Kina da Ubangida a cikin masana’antar?
Eh! Ina da iyayen gida da yawa a cikin masana’antar, kin ga kamar Abora Shika, Action Director, Aminu AKG, Mansur Khan, da dai sauransu.
Wace ce babbar kawarki a cikin masana’anatar kannywood, kuma kafin ki fara fim wace ce ta fi burge ki da har ta zama allon kwaikwayonki, shin kun hadu da ita bayan shigarki, ko kun yi fim tare ko kuwa har yanzu tukunna dai?
Gaskiya Adaman Kamaye, ita ce wadda take burge ni, kuma cikin hukuncin ubangiji sai ga shi an harhada mu ayyuka da ita.
Ya alakarki take da sauran abokan aikinki?
Ina da kyakkyawar alaka da kowa.
Gari nawa kika taba zuwa ta dalilin flm?
Na taba zuwa Jigawa, na taba zuwa Keffi, na je Abuja, na je da dama dai.
Wanne irin abinci da abin sha, da kuma kayan sakawa kika fi so?
Shinkafa da wake, sai Kok, sai kuma doguwar riga.
Kafin shigarki fim, ko akwai abin da ya fara baki tsoro game da masana’antar, kamar misali; irin yawan maganganun da ake yi akan ‘yan fim da sauransu?
Tsakani da Allah ko dazu na ji maganar da ta tsorata ni a kan sana’ar, amma na dai daure da sauransu, don mijina da na fita a hannunsa na je Zariya na ga yarana, sai na shiga falonsa da niyyar na gaishe shi, yake ce min; ina bar wa yarana abin magana, haka kawai ina zaune na fada harkar fim, don duk a cikin garin zariya wanda yake da babbar waya yana da hotona, yana da fim dina, har a kasuwa ake kunnawa. Sai na ce masa, ni dama na shiga sana’ar ne don a ganni kuma a nuna ni ne, amma kuma tsakani da Allah abin ya tsorata ni, na tsorata matuka gaskiya.
Misali; Yanzu a ce mijinki ya ce zai maida ke gidansa, shin za ki yarda ki amince har ki koma ki hakura da fim din ko kuwa ya ki ke gani?
Gaskiya ba yadda za a yi ya ce zai maida ni din ne shi ya sa, kamar fa ni ce matarsa ta hudu, ni ce Amaryarsu. Bayan na fita daga gidansa kuma ya kara yin wani auren, to kin ga matan sun riga sun zama guda hudu, sai dai ba mu san abin da Allah zai yi nan gaba ba.
Mene ne burinki na gaba game da fim?
Burina wallahi yadda nake a yanzu haka, Allah ya fito min da miji ya ce; “Amina gobe a daura aure”, da gudu za a daura auren nan, na hakura da fim. Daman kin san abin da Hausawa suke cewa ‘Wai a rashin uwa – akan yi uwar daki’. Don gaskiya na sassamu ma mijin a haka, amma kin san yanzu aure ba a yin sa da ka, sai ka bincika waye mijin, wanne gida zai kai ka, da sauransu. Kawai irin wadannan matsalolin ake samu, amma burina da fim shi ne; ko yau Allah ya fito mun da miji to fa na hakura da fim har ga Allah.
Me za ki ce game da irin kallon da ake yi wa ‘yan fim na cewar ba sa iya zaman aure, ko kuma idan suka yi auren suna iya ci gaba da yin fim kamar ba zaman aure suke yi ba?
Eh to, abin da zan janyo hankalin mutane shi ne, kin ga kamar fim mutane da dama suna yi masa wata irin fahimta, don wallahi sai a zaci irin ‘yar fim muguwar shahararriyar ‘yar iska ce, ko wacce ta bujirewa iyayenta, har ga Allah ni ma a da kafin na shiga ina da jahilci abin, amma da na shiga sai na ga abin ba haka ba ne, tun da ni gaskiya tun da na fara fim ni ban taba jin wanda ya yi min a cikin maza ko irin manyanmu dai haka su Daraktocinmu, ko Furodusas, a ce wai wani ya yi mun tayin maganar banza ba, gaskiya ban samu wannan matsalar ba. To kuma shi aure kaddara ce mata nawa ne ba sa yin fim suke yin aure kuma ya mutu, ko ni lokacin da aure na ya mutu, ko ‘workers fast’ ban taba yi ba, na yi auren, auren ya mutu. to kin gani sai a ce wai ba a zaman aure, ba ma duba cewar kaddara ce tana rubuce cikin littafin kaddarar mutum. Don haka kawai abin da zan ce Allah ubangiji wadanda suka yi Allah ya zaunar da su, wadanda ba su yi ba ubangiji Allah ya fito musu da da nagari. Ni mutum daya ne ma na taba ji Alhaji Asabe Olala, muna da wata Antis G, da take Dadin Kowa, shi ne ya ke cewa yana so ya kafa tarihi ya aureta kuma su ci gaba da fim, to kuma ma Allah bai yi ba.
Ya za ki yi wa masu karatu bayanin yadda ku ke fita aiki, da yadda ku ke komawa gida?
Yadda muke fita aiki shi ne; Kamar yanzu mutum ya kira ka aiki irin ya rage kamar saura kwana uku, biyar zai fada miki kamar misali, za a fita aiki na ranar Lahadi misalin karfe takwas, idan kika fita wajen aikin a nan za ku hadu, sannan za ki karbi fim din a rubuce ki karanta ki ga wuri nawa za ki fito, bayan kin ga nawa za ki yi, ba wani lokacin komawa kawai kana gama yin naka za ka tafi gida, haka abin yake. In kuma ka ga za ka iya tsayawa ka ci gaba da kallo to ba wata matsala. Shi ne dai abin da ni na sani nake ganin za su fahimta, ko karfe goma mutum ya ce, duk dai lokacin da aka kira ya danganta da yanayin lokacin da aka saka. To, akwai kuma wadansu da dama da basa son irin cunkoso, idan kawai ki ka ga an daga waya an kira ki to ya rage kamar minti biyar ko goma a fara aikinka sai a kira ka a waya za ka je wajen idan har a kusa ka ke, wasu kuma kawai duk wanda ya ke ciki ya yi niyya zai iya zuwa in an yi aikinsa a lokacin to, in ba a yi aikinsa ba kuma washegari zai iya dawowa.
Ta wacce hanya kike ganin za a bi domin a rinka wayar da kan al’umma, musamman masu kallon fina-finan Hausa, wajen yi wa ‘yan fim kyakkyawan kallo?
Hanyar da za a bi ita ce kamar irin bangarenku da kuma wanda yake gani kamar sana’ar ba ta yi ba, in Allah yayi yana da abinci a ciki shi ma idan ya shiga zai gane cewar ba ta da matsala.
Wanne kira za ki yi ga masu kokarin shiga harkar fim?
Kiran da zan yi ga duk wanda zai shiga shi ne, Ya dauke ta sana’a ko da yake ita duk yadda ka dauke ta a haka za ta zo maka, amma dai mutum ya shiga da niyyar zai shiga sana’a, Allah kuma zai taimake shi a kai.
Me za ki ce da masu kallon fina-finanki?
Babu abin da zan ce musu da ya wuce godiya, mun gode mun gode Allah ya kara kauna.
Me za ki ce da makaranta shafin Rumbun Nishadi?
Su ci gaba da neman Jaridar domin karanta labarai na gaskiya musamman a wannan bangare, su ji gaskiyar zance daga bakin me shi.
Me za ki ce da ita kanta jaridar LEADERSHIP HAUSA?
Gaskiya hirar ta mun dadi sosai, ina addu’ar wannan jarida Allah ya kara daukakata ya ja kwana, Amin.
Ko kina da wadanda za ki gaisar?
Babbar gaisuwata ina gaida mahaifiyata Khadija, sannan ina gaishe da Adaman Kamaye, don gaskiya ba abin da zan cewa Adama don tana son ci gabana matuka, sannan kuma sai su Daraktocinmu gabaki daya ina gaida su, ina gaida Ai, Zulaiha, da Hassana.