Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya tabbatar da aniyar gwamnatin sa ta ci gaba da haɗa kai da Hukumar Kai Agajin Gaggawa ta Ƙasa (NEMA) wajen inganta tsarin daƙile bala’o’i da haɗurra a faɗin jihar.
A wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sulaiman Bala Idris, ya fitar ranar Litinin, 13 ga watan Oktoba, tn bayyana cewa Gwamna Lawal ya halarci bikin Ranar Ƙasa da Ƙasa ta Rage Haɗarin Bala’o’i ta shekarar 2025, da kuma ƙaddamar da sabbin tsare-tsare da suka shafi wannan fanni, wanda aka gudanar a cibiyar taro ta NAF da ke Abuja.
A wajen taron, Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, GCON, ne ya jagoranci ƙaddamar da Shirin Tsare-Tsaren NEMA na Shekaru Biyar (2025–2029), da Manufar Rage Haɗarin Bala’o’i (2025–2030), da kuma Shirin Ayyuka na Shekaru Uku (2025–2028), ƙarƙashin taken: “Fund Resilience, Not Disaster” – wato, kuɗaɗe su tallafa wa juriya, ba bala’o’i ba.
A jawabin sa, Gwamna Lawal, ya yaba wa NEMA bisa shirya wannan muhimmin taro da kuma jajircewarsu wajen gina tsarin rage haɗarin bala’o’i a Nijeriya.
Ya ce, “Bala’o’i kan zo cikin tsarin da ke jawo juna — bala’i ɗaya na iya haifar da wani. Wannan ya nuna cewa babu haɗari da ke zaman kansa; duk suna da alaƙa da juna, kuma magance su na buƙatar tsari mai ma’ana da haɗin kai.”
Gwamnan ya ƙara da cewa, yayin da aka ƙaddamar da wannan sabon shiri na shekaru biyar, akwai buƙatar kowane ɓangare ya zurfafa haɗin gwiwa, domin a tabbatar da cewa babu wanda aka bari a baya wajen gina ƙasa mai juriya da aminci.
A cewar sa, taken bana na “Fund Resilience, Not Disasters” ya zama wajibi a juya shi zuwa tsare-tsare na zahiri da za su tabbatar da ɗorewar kuɗaɗen da ake warewa don kula da bala’o’i, ganin cewa wannan fanni yana ta canjawa lokaci zuwa lokaci.
Gwamna Lawal ya kuma bayyana irin ƙalubalen da Jihar Zamfara ke fuskanta, ciki har da matsalar tsaro, gobara, ambaliyar ruwa, ruftawar ramin haƙar ma’adinai, da sauran tasirin sauyin yanayi. Duk da haka, ya yaba wa NEMA bisa kasancewa tamkar ginshiƙi wajen tallafa wa jihar a duk lokacin da ake fuskantar irin waɗannan matsaloli.
Ya ce, “Mun ƙarfafa hukumar mu ta Zamfara Emergency Management Agency (ZEMA) da ƙarin iko domin inganta amsawa kiran gaggawa ga bala’o’i. Muna kuma haɗa tsarin kula da haɗurra cikin tafiyar da gwamnati ta hanyar gargaɗi da wuri, haɗin kai da al’umma, da gyaran cibiyoyi — domin mu yi imani cewa juriya mai ɗorewa tana farawa daga matakin jiha.”
A ƙarshe, Gwamna Lawal ya miƙa godiya ga Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu, GCFR, bisa jagorancinsa a waɗannan lokutan ƙalubale, tare da gode wa Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, GCON, da kuma Darakta Janar ta NEMA, Hajiya Zubaida Umar, bisa haɗin gwiwa da taimako da suke bai wa Zamfara don fuskantar matsalolinta.