Assalamu alaikum masu karatu, barkammu da sake haduwa da ku a wannan makon a cikin shirin namu na Ado Da Kwalliya, inda za mu yi magana yau akan kula da tafin hannu, laushin tafin hannu ga mace yana da muhimmanci sosai kamar yadda bushewarsa take kawo matsala, za ki ga lokacin sanyi hannu yana yawan bushewa saboda aikin gida da muke yi, muna yawan sa hannu a ruwa, kamar su wanke-wanke ko girki za ki yi dole hannunki kina sa shi a ruwa kina fitarwa saboda yanka wancan wanke wancan haka dai har ki gama ko yaushe hannu a ruwa saboda ruwa ne abokin aiki don haka sai ki ga lokacin sanyi hannu yana yawan bushewa.
To ga yadda za ki yi hannunki ba zai na yawan bushewa ba:
Abubuwan da za ki tanada:
Man Zaitun, Gishiri, Turaran Miski, Lemon Zaki, Suga, Bota.
Kullum bayan kin gama aiki sai ki hada man zaitun da gishiri kadan ki rika shafawa sau daya ko sau biyu a rana, ki hada suga da Bota daidai misali ki rika murzawa hannuwanki ya yi kamar minti 10 ki matse ruwan lemon tsami da man zaitun ki rinka shafawa a hannunki ki hada gishiri da turaran miski da lemon zaki ki rika shafawa kowane dare. Da yarda Allah hannuwanki zai yi laushi ya yi kyau ba zai yawan bushewa ba za ki ga ya yi kamar ba lokacin sanyi ba.